Connect with us

Uncategorized

Dalilin da ya sa na kara ga Kujerar Sarautan Kano – Ganduje

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana dalilin da ya sa ya kara kujerar Sarauta 4 a Jihar Kano.

Naija News Hausa na da sanin cewa Sarki Muhammad Sanusi II ne ke wakilcin dukan Jihar Kano a matsayin Sarki a da, kamar yadda muka sanar a baya, Gwamna Ganduje ya saken tsarin Sarautan Jihar, ya kuma mayar da ita kujerar Sarauta 5.

Wannan ya faru ne a ranar Laraba da ta wuce, bisa amincewar Gidan Majalisar Wakilan Jihar Kano da Gwamnan da rabar da kujerar Sarautan daga guda zuwa biyar.

Ko da shike mutane na zargin cewa Ganduje yayi hakan ne don rage karfi da Ikon mai martaba, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Gwamna Ganduje ya mayar da martani ga wanan zancen, ya ce “Duk masu zargi da fadin cewa yayi hakan ne don Sanusi na iya ci gaba da furtan yawun su. Mu dai kokarin mu ita ce mu kai Jihar Kano a gaba (Next Level)” inji shi.

“Kokarin mu ita ce don kai Jihar Kano gaba, musanman akwai bukatar hadin kan sarakai don ci gaban Ilimi, Tsaro da kuma yaduwar Hatsi a Jihar Kano” Ganduje.

“Mutanen Jihar Kano sun yi murna da wannan, zamu kuma tabbatar da cewa sabin Sarakan sun jawo ci gaba a Jihar Kano wajen shugabancin su”

Wannan ita ce bayanin Ganduje a zaman Kungiyar Gwamnonin Kasar Najeriya da suka yi a birnin Tarayyar, Abuja.

KARANTA WANNAN: Takaitaccen Labarin Rayuwar Maryam Booth