Connect with us

Labaran Najeriya

Ji Abinda Atiku yace zai yi Idan har Kotun Karar Zabe ta hana shi Kujerar Mulkin Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, da kuma dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana da cewa lallai zai amince da duk matakin da Kotun Kara ta gabatar a karar shi da shugaba Muhammadu Buhari, a kan sakamakon zaben 2019 da aka kamala a baya.

“Ba zani dauki alhakin zubar da jinin ‘yan Najeriya ba, ba zani kuma bude ido da ganin Najeriya ta shiga wata farmaki ba.”

Wannan ita ce bayanin Atiku a wata sanarwa da ya bayar daga bakin kakakin yada yawun sa ga hidimar neman zabe, Segun Sowunmi.

Atiku yayi bugun gaba da cewa ba zai bar Najeriya ta sake fuskantar wata mawuyacin hali ba don yana neman kujerar shugabancin kasar, cewa zai amince da duk matakin karshe da Kotu zata gabatar a karar shi da Buhari.

“Muna zato da kuma addu’ar ganin cewa Najeriya ta wanku daga duk wata yanayi da ake cikinta, musanman, cin hanci da rashawa, rashin bayyana gaskiya ga lamarin kasa, son kai, muzunta wa juna da kuma ta’addanci” inji bayani Sowunmi a cikin gabatarwan.

“Ya saura ga Kotun Kara da kadamar da gaskiya a karar su. Muna kuma diban cewa Kotun zata gudanar da aikin su yadda ya kamata. Mutane na jira da fatan alkhairi ga karar karshe, mu kuma muna shirye don karban duk wata mataki da aka dauka ta karshe akan karar”

“Ko da shike, ba yadda za a janye daga gaskiyar cewa Atiku ne ya lashe zaben shugaban kasa ta 2019. Mutane na da tabbacin haka, kuma tarihi da bincike ta nuna hakan” inji Sowunmi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa, Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC), ya gabatar da wata zargi akan Lektarorin Manyar Makarantar Jami’ar Kasa.

Farfesa Attahiru ya ce “A ganewa na, na kula da cewa matsalar da kasar mu ta Najeriya ke fuskanta ya kasance ne sakamakon yadda aka kada darajan dimokradiyya a kasar, musanman yadda masu karfi suka raunana hidimar zaben kasar”.