Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 10 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau
advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 10 ga Watan Mayu, 2019

1. Shugaba Buhari ya nada Emefiele a matsayin sabon Gwamnan Banking Najeriya (CBN)

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake zaben Mista Godwin Emefiele a karo ta biyu a matsayin Gwamnan Bankin Tarayyar kasar Najeriya (CBN).

Naija News ta fahimta da hakan ne bisa wata sanarwa da aka bayar cewa shugaba Buhari ya rattaba hannu ga wata takarda na sake zaben Mista Emefiele.

2. Kotun Neman Yanci ta gabatar da Oyetola a matsayin Gwamnan Jihar Osun

Kotun Neman Yanci, bayan jayayya da bincike akan hidimar zaben 2018 ta kujerar Gwamnan Jihar Osun, ta bada yanci ga Gboyega Oyetola da  zama Gwamnan Jihar Osun.

Gidan Labaran nan ta mu ta gane da hakan ne bayan da Alkalin da ke jagorancin karar, Hannatu Sankey, a ranar Alhamis da ta gabata, ta gabatar da Oyetola a matsayin Gwamnan Jihar.

3. Dalilin da ya sa Buhari ba zai iya dakatar da ni ga tseren shugabancin Majalisa ba – Ndume

Mohammed Ali Ndume, Dan takaran kujerar shugabancin Gidan Majalisar Dattijai, ya fada cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai iya dakatar da shi ga tseren neman kujerar Gidan Majalisar ba.

“Shugaba Buhari ya bada gaskiya ga Dimokradiyya, saboda haka, ba zai so ya kafa baki ga hidimar zaben gidan Majalisar ba” inji Ndume.

4. Shugaba Buhari ya gana da Shugabannan Hukumomin Tsaron Najeriya

A ranar Alhamis da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya yi zaman tattaunawa da Manyan Shugabannan Hukumomin Tsaron Najeriya, hade da jagoran hukumar ‘yan sandan, IGP Muhammed Adamu.

Naija News Hausa ta gane da cewa shugaba Buhari yayi ganawar ne da Shugabanan Tsaron bayan wata ganawa da yayi da dukan hukumomin tsaron kasar a ranar Talata da ta wuce.

5. Ban Amince da Matakin Kotun Neman Yanci ba – Adeleke

Dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Osun daga Jam’iyyar PDP a zaben 2018 da aka yi shekarar baya, Sanata Ademola Adeleke, yace bai amince da matakin Kotun Neman Yanci ba da gabatar da Gboyega Oyetola a matsayin Gwamnan Jihar Osun.

Adeleke ya fadi hakan ne bayan da Kotun ta gabatar da Oyetola a ranar Alhamis da ta wuce.

6. IGP Adamu ya gargadi Jami’an Tsaro akan Kashe-Kashen da ake a Kasar Najeriya

Shugaban Jami’a Tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Adamu Mohammed yayi kiran gargadi ga rukunonin ‘yan sandan Najeriya hade da ‘yan tsaro da yaki da barari da ‘yan gungume (SARS), cewa su tuna da cewa aikin su shine tsare al’ummar Najeriya.

Wannan bayanin IGP Adamu ya biyo ne bayan wata ganawan tattaunawa akan tsaron kasa da shugaban ya yi da Gidan Majalisar Dattijai.

7. Za a yi zaben shugaban Gidan Majalisar Dattijai ne bisa kuri’ar boye – Gaya

Jagoran Hidimar zaben Shugaban Gidan Majalisar Dattijai ta 9, Sanata Kabiru Gaya, daga karkashin Jam’iyyar APC ta Kano, ya bayyana da cewa zaben shugaban Gidan Majalisar zai kasance ne kan zaben boye.

Naija News Hausa ta gane da cewa Gaya ya fadi hakan ne don mayar da martani ga zancen wasu da ke kokarin shiga lamarin shugabancin Majalisar.

8. Kotun Neman Yanci zata Kadamar da Shari’a a kan Onnoghen a yau

A yau Jumma’a, 10 ga watan Mayu 2019, Kotun Neman Yanci zata kafa baki ga Karshe Karar da ake akan tsohon shugaban Alkalan Najeriya da aka dakatar a baya, Walter Onnoghen.

An gabatar ne da hakan a wata sanarwa da aka bayar ranar Alhamis da ta wuce daga bakin Sa’adatu Musa Kachalla, kakakin yada yawun kotun.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com