Connect with us

Uncategorized

Mutane Ukku sun Mutu, an Kuma Ribato 5 a Kihewar wata Jirgin Ruwa a Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata hadarin Jirgin Ruwa ta dauke rayukar mutane 3 a shiyar kauyan Tudun Wada, wata karamar hukuma a Jihar Kano.

Naija News ta fahimta da cewa hadarin ta faru ne a yayin da jirgin ruwa ke dauke da mutane Takwas daga Kayya zuwa shiyar Jogana, a karamar hukumar Tudun Wada.

Ofisan Yada Yawun Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar Kano (PPRO), DSP Abdullahi Haruna, ya bada tabbacin hakan a wata sanarwa da ya bayar a ranar Alhamis a garin Kano.

DSP Haruna ya bayyana da cewa hukumar su ta karbi kirar gaugawa a ranar 7 ga wata Mayu, misallin karfe 5 na safiya cewa wata jirgin ruwa ta Kihe da mutane 8 a cikinta.

“An samu ribato rayuka 5 daga hadarin jirgin ruwan, Ukku kuma sun riga sun mutu kamin isar mutane a wajen.” inji shi.

Sunayan mutane ukku da suka mutu a hadarin jirgin ruwa ne haka; Ashiru Hamisu, mai shekaru 27 da haifuwa, Ibrahim Tasi’u dan shekaru 45, da kuma Buhari Basiru mai shekaru 23.

DSP Haruna ya bayyana da cewa dukan su kuma ‘yan kauyan Fankanoki ne.

“A halin yanzu, hukumar ma na kan bincike don gane matsala da kuma mafarin kihewar jirgin ruwan.”