Connect with us

Labaran Nishadi

Karshen Zamani: An Kame wani Tsoho Mai Shekaru 72 da ke yiwa ‘yan makaranta fyade

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News ta gane da wani Tsoho da aka sanar da ke yiwa kananan ‘yan makarantan Sakandiri biyu fyade a yankin Isogbo ta Jihar Osun.

An bayyana da cewa tsohon, mai shekaru 72 da haifuwa na kwanci kusan kullum da ‘yan makarantan sakandiri da ke a makarantar, da cewa ‘yan matan kan fita ne daga ajinsu a lokacin da sauran ‘yan makaranta ke cikin koyaswa, su kuma kara gaba zuwa gidan tsohon kullum don kwanci da shi.

An yi nasara da kame tsohon ne bayan da wani mazaunin unguwar ya gane da jin motsi da kuma ji tsuwa na fita daga dakin tsohon, garin bincike da leken ko menene ke faruwa, sai ya gane da cewa tsohon ne ke yin jima’i da kananan yaran.

Da ganin hakan sai ya yi wuf da kiran mutanen unguwa, daga nan kuma sai suka ja shi zuwa ga Jami’an tsaro don bashi girman tsufar shekaru.

Da aka bincike shi, ya bayyana da cewa yana da kananan ‘yan mata fiye da 10 da yake kwanci dasu.

“Ina da ‘yan mata kanana fiye da 10 da ke ziyara na a kullum don kwanci da su” inji shi.

Ko da shike ba a bayyana sunan tsohon ba, amma a halin yanzu yana a dakile wajen Jami’an tsaro, a yayin da ake kara bincike akan lamarin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Wani mutumi mai suna Umar Bello daga shiyar Wurro-Chekke ta birnin Yola, a Jihar Adamawa, ya bayyana ga Kotun Kara dalilin da ya sa ya tashi yiwa wata ‘yar yarinya fyade.

KARANTA WANNAN KUMA: Ali ArtWork (Madagwal) Na cikin Mawuyacin Hali