Connect with us

Uncategorized

Allah Abin Godiya! Yara marasa Iyaye sun kuri Mutuwa a wata Gobarar Wuta

Published

on

at

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa wata gobarar wuta da ya faru a ranar 7 ga Watan Mayu ya tashi konewa da yara mara sa iyaye da ake nunawa kulawa a Jihar Kogi.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, abin ya faru ne a hanyar Agala Ate ta shiyar Aniygba, a Jihar Kogi.

An bayyana da cewa yaran na cikin dakin bacin su a yayin da dakin ya kame da gobarar wuta. Biyu daga cikin yaran, Mercy da Jeminah sun samu ganewa kamun wutan, da ganin hakan sai suka yi wuf suka hari dakin Shugaban da ke kulawa da su.

Ko da shike ba wanda ya mutu a gobarar wuta, Gidan ya kone daga sama har kasa, amma an bayyana da cewa yara shidda sun rasa kayakin sawar su a gobarar wutan.

Gidan Kulawa da yara mara iyayen sun yi kira ga Al’ummar Najeriya duka da taimaka masu da kayakin sawa da kayakin zama da za a ci gaba da kula da yaran da ita.

KARANTA WANNAN; Ali ArtWork (Madagwal) Na cikin Mawuyacin Hali Rashin Lafiya