Uncategorized
Hauka Ko Zafin Zucciya? Wani mutum a Jihar Neja, ya kashe Makwabcin sa da saran Adda
A ranar Lahadi da ta gabata, manema labarai sun gano da wani mai suna Garba Sani da Jami’an tsaro suka kame da zargin kashe makwabcin sa da saran Adda.
Naija News Hausa ta samu fahimtar cewa Garba ya kashe makwabcin sa, Nura Mallam, da saran adda ne a wata gari da ke da suna Shantali Dukku, a karamar hukumar Rijau ta Jihar Neja.
An bayyana ne da cewa babban mutumin, Maje Mallam ne ya kai wannan karar ga Ofishin Jami’an tsaron ‘yan Sandan yankin Rijau game da abin da Sani ya aikata.
Bisa binciken manema labarai, an iya gane da cewa matashin da ke da shekarun haifuwa 33, ya daddace Nura ne da saran adduna har ga mutuwa.
“Na kashe Nura ne da saran Adda a kan jayayya da ke tsakani na da shi tun da baya” inji Sani.
Ya kara da cewa lallai yayi hakan ne don ya gane da cewa Nura a kowace lokaci da magana ta hada su, sai kawai Nura ya dingi zagin sa da kuma yi masa ba’a cikin mutane.
“Lokatai da dama na gargadi Nura da barin hakan, amma sai bai bari ba”
“A farko gaskiya bani da muradin kashe shi, amma da na fusata sai na yi hakan. bani da wata abin da zan iya fada kuma” inji shi.
Muhammad Abubakar, Ofisan Yada yawun Jami’a Tsaron Yankin, ya bayyana da cewa lallai ba wata wai, hukumar zata kai shi har gaban Kotu.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wani mutum mai Tabuwar kwakwalwa ya kashe Dan Sanda a Jihar Kwara.