Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 13 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 13 ga Watan Mayu, 2019

1. Gurin Shugaba Buhari ita ce ganin ci gaba ‘yan Najeriya da kasar – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana da cewa gurin shugaba Muhammadu Buhari ga ‘yan Najeriya da talakawan kasar Najeriya duka ita ce, ganin cewa kasar da al’ummar ta ta samu ci gaba ko ta ina.

Naija News Hausa ta gane da cewa shugaban ya fadi hakan ne a wata sanarwa da aka bayar ranar Asabar, 11 ga watan Mayu da ta gabata.

2. Tinubu zai dauki shugabancin kasar Najeriya baya Buhari, Ba kuma wanda zai iya tsare shi – APC

Wani Jigon Jam’iyyar shugabancin kasar Najeriya, APC, Oludare Falade, ya bayyana da cewa shugaban Jam’iyyar APC na Tarayyar kasar Najeriya, Bola Tinubu zai dauki kujerar shugabancin kasar Najeriya, bayan saukar Buhari a shekarar 2023, kuma ba wanda ya isa ya dakatar da shi, inji shi.

Wannan bayani ta fito ne daga bakin Mista Falade, Ciyaman na Jam’iyyar Mega Progressives Peoples Party (MPPP), da aka komar da Mega Party of Nigeria (MPN), cewa Tinubu zai samu goyon bayan ‘yan Najeriya da shugabancin kasar Najeriya a shekarar 2023.

3. Yadda Oshiomhole ya tsige ne da hadin kan Hukumar DSS – Okorocha

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha ya zargi Ciyaman na Jam’iyyar APC na Tarayya, Adams Oshiomhole, da amfani da Hukumar Tsaron DSS don ci masa mutunci.

Okorocha ya bayyana a wata ganawa da manema labarai da cewa Adams ya kore shi daga gidansa da amfani da Hukumar DSS a lokacin da ya ziyarce shi a gidansa.

4. Hukumomin Tsaro sun Katange gidan Sanusi, Sarkin Kano

Manema labarai sun sami sani da cewa an tura Jami’an tsaro don katange fadar Mai Martaba, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Naija News ta gane da hakan ne bisa wata rahoto da manema labaran Daily Trust suka sanar, cewa kimanin motar Hilux 10 ne aka taras a fadar sakin Kano, cike da Jami’an tsaro, a ranar 11 ga watan Mayu.

5. Majalisar Dattijai sun mika Kasafin kasar Najeriya ta 2019 ga shugaba Buhari

Gidan Majalisar Dattijai sun bayyar da takardan kasafin kudin Najeriya ta shekarar 2019 ga shugaba Muhammadu Buhari don bincike a kai.

Naija News Hausa ta gane da cewa gidan Majalisar Dokoki da ta Wakilai ne suka amince da bayar da kasafin kudin a ranar 30 ga watan Afrilu ta shekarar 2019.

6. Saraki ya Kalubalanci Hukumar EFCC da kwace masa Gida zaman sa

Shugaban Gidan Majalisar Dattijai, Bukola Saraki ya bayyana rashin amincewar sa da matakin Hukumar EFCC ga kwace gidansa da ke a Ikoyi, Jihar Legas.

Wannan ya faru ne bayan da Hukumar EFCC suka kafa kai ga binciken Saraki da wata zargi.

7. Birkicewa a Jam’iyyar APC akan Sabon Rukunin Shugaba Buhari

Rikici a da Birkicewa a Jam’iyyar APC, a yayin da ake cece kuce game da wadanda zasu zama ministoci a sabon rukunin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari ta karo na biyu.

Babu ganewa da fahimta tsakanin shugabannan Jam’iyyar APC akan gurin shugaba Buhari ga shugabancin sa ta karo na biyu.

8. An Samar da Dakarun Tsaro fiye da 500 a Masujadai da ke a Jihar Borno.

Kimanin Dakarun Tsaron Najeriya da hadewar Hukumar Civil Defence (NSCDC) 500 ne aka watsar a Jihar Borno don kare mutane daga hari a masujadai.

Naija News ta fahimta da cewa an yi hakan ne don karfafa tsaro da kumar neman tsare rayukan mutane a wannan lokaci da ake ciki, musanman Watan Ramadani.

9. Manchester City ta lashe Kofin Nasarar wasan Kwallon Ingila
Bayan Gwagwarmaya da yawar wasanni a tseren wasan Kwallon Kafa ta Ingila, Kungiyar wasan Kwallon kafa ta Ingila ta kai ga cin nasara lashe tseren wasa.

Bisa ga wasan karshe ta Kofin Ingila da aka yi a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu da ta wuce, Manchester City sun nuna mazantaka, sun kuma dauki kofin wasan da gwalagwalai 4-1 ga wasan.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com