Connect with us

Uncategorized

Gwamnan Kano, Ganduje ya Mika Sandar Ikon Jagoranci ga Sabbin Sarakan Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Lahadi da ta wuce, Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano, ya mika Alkibba da Sandar Shugabanci ga sabbin Sarakai hudu da ya nada a Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Abdullahi Ganduje ya karar kujerar Saurata Hudu a Jihar Kano.

Gidan Labaran nan tamu na da fahimtar cewa Ganduje ya rabar da Kananan hukumomin Jihar Kano ne ga Kujerar Sarauta 5 da Jihar ke da ita.

Jihar Kano na da kananan hukumomi 44 ne, a cikin ta aka baiwa Mai Martaba, Muhammad Sanusi II, kananan hukumomi 10. Sauran hukumomin kuma aka rabar ga sauran Sarakan.

Ga sunayan Sabbin Sarakan da kuma inda zasu jagoranta kamar haka;

  1. Aminu Ado-Bayero – zai jagoranci Bichi Emirate
  2. Tafida Ila                 – zai jagoranci Rano Emirate
  3. Ibrahim Abdulkadir – Zai jagoranci Gaya Emirate
  4. Ibrahim Abubakar ll – Zai jagoranci Karaye Emirate

Naija News Hausa ta samu ganewa da cewa Ganduje ya bayar ne da takardan jagoranci ga Sarakan tun ranar Asabar da ta wuce, ko da shike ana zancen cewa Kotu ta kalubalanci Ganduje da hakan, amma ya bayyana da cewa bai san da matakin Kotu ba.