Uncategorized
Bidiyo: Kalli Mama Taraba Bayan da aka yi Mata Tiyata
Tsohon Ministan Harkokin Matan Najeriya, Sanata Jummai Alhassan, da aka fi sani da suna Mama Taraba, ta nuna godiyan ta ga ‘yan uwa da masoya da addu’a da aka yi mata a lokacin da aka yi mata aikin tiyatan gwiwa.
Mama Taraba a wata sanarwa da aka bayar a baya ranar 17 ga watan Mayu 2019, ta nemi bukatar addu’a daga ‘yan Najeriya duka akan tiyata da taken shirin yi a lokacin.
Sai ga shi a ranar Litini, 13 ga watan Mayu da ta wuce, Mama Taraba ta aika sakon murna da bayyana ga al’ummar Najeriya da cewa Tiyatan da aka yi mata ya tafi yadda ya kamata, kuma ta fara samun sauki.
A cikin sakon ta, Ta ce; “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! aikin Tiyata da na tafi ya tabbata yadda kamata, gashi kuma kulllum sai karuwa nike da samun sauki”
“Nagode maku duka da addu’o’in ku, ‘Yan Uwa, Abokan Arziki da dukan ‘yan Najeriya Masoya duka.” Nagode sosai sosai.” inji Mama Taraba.
https://twitter.com/SenAishaAlhassn/status/1127858201632878592
Ko da shike Mama Taraba bata bayyana ko ina ne take ba, amma ta sakon ta da biyon da ta aika ya nuna alamar samun sauki.
Ka tuna da cewa Sanata Jummai ta janye kwanakin baya daga Jam’iyyar APC ta kuma koma ga Jam’iyyar UDP bayan da ta kasa ga cinma gurin ta na takara a Jam’iyyar.
KARANTA WANNAN KUMA; Hauka Ko Zafin Zucciya? Wani mutum a Jihar Neja, ya kashe Makwabcin sa da saran Adda