Connect with us

Labaran Najeriya

APC/PDP: Ku bar yi mani ba’a, Zan barranta kujerar Mulki Idan Atiku ya ci kara a Kotu – Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wata gargadi mai karfin gaske da Shahararrun ‘yan wasan Kwaikwayo da Ban Dariya na Najeriya, cewa su janye daga yi masa ba’a wajen hidimar su.

“Ku bar yin ba’a da ni, sauran kasashen waje na da tasu matsalar da suke fuskanta a kasar su. Amma ba zaku taba gan suna yin ba’a ga shugabanan su ba” inji Buhari.

Naija News Hausa ta gane da bayanin shugaba Buhari ne a wata gabatarwa da ya bayar a ranar Litini, 13 ga watan Mayu da ta wuce a birnin Tarayyar kasar Najeriya, Abuja.

Shugaba Muhammadu ya kara da cewa yana shirye don barrantar da kujerar mulkin sa idan Kotun karar Zabe ta bayyana Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP a matsayin mai nasara ga hidimar zaben 2019.

“Gwamnati na na kokarin ganin cewa an magance matsalar tsaro da ake ciki a kasar Najeriya a wannan lokaci, don wannan ne babban matsalar da kasar ke fuskanta” inji Buhari.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a ranar 7 ga Watan Mayu 2019, cewa wasu ‘yan zanga-zanga sun katange mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a babban hanyar Umaru Musa Yar’Adua ta birnin Abuja.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, mazaunan kauyan, watau Gwarawa (Gbagyi) sun keta manyan hanyoyin ne da ta bi zuwa filin jirgin sama ta birnin Abuja don nuna rashin amincewar su akan tawaye da muzuntasu da Sojoji suka yi na maye Filayen su da suka gada.