Connect with us

Uncategorized

Wani ya caka wa Malaman Asibiti wuka don ta hana shi Kwanci da Ita a Jihar Kano

Published

on

at

advertisement

A ranar Litini da ta gabata, Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya sun kame wani mai suna Bashir Yahaya, mazaunin Kabuga quarters, da laifin caka wa wata Malamar Asibiti, Aisha Kabir wuka a wuya wai don ta hana shi kwanci da ita.

Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai, Aisha Kabir ta hana Bashir, dan matashin mai shekaru 20 ga haifuwa jimma’i ne da ita, bayan da yayi ta kokarin hakan sau da yawa tana kuma hana shi, kwaram sai ya caka mata wuka a wuya.

Wannan abin ya faru ne a wata Asibiti da ke a Tal’udu quarters, a karamar hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar, DSP Abdullahi Haruna, ya bada tabbacin hakan ga manema labarai.

A bayanin sa, ya ce “Hukumar ‘Yan Tsaron yankin Gwale ta karbi kirar gaugawa a ranar 12 ga watan Mayu 2019, a missalin karfe 7pm na maraice da cewa An caka wa wata Malaman Asibiti wuka a Asibitin da ke a Tal’udu quarters”

“Da jin hakan, Jami’an tsaron sun hari wajen don kama matashin da ya aiwatar da mugun halin, aka kuma kai Aisha Kabir a asibin Murtala Muhammed Specialist Hospital, ta Kano don nuna mata kulawa ga wuyar ta da Bashir ya caka wa wuka.”

DSP Haruna ya ci gaba da cewa Jami’an tsaro sun iske Bashir da zubar jini a jikinsa da kuma wukar da yayi amfani da shi ga wuyan Aisha.

“A halin yanzu Bashir na a kulle a Ofishin Jami’an tsaron yankin, ya riga ya amince da zargin da ake yi a gareshi kuma za a kai shi a Kotu bayan an gama hakan”

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa cewa An Kame wani Tsoho Mai Shekaru 72 da ke yiwa kananan ‘yan makaranta fyade.

Da aka bincike shi, ya bayyana da cewa yana da kananan ‘yan mata fiye da 10 da yake kwanci dasu.

“Ina da ‘yan mata kanana fiye da 10 da ke ziyara na a kullum don kwanci da su” inji tsohon.

Ko da shike mutanen shiyar sun tashi yi masa duka amma an mika shi ga Jami’an tsaro don diban tsufar sa.