Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Kotu ta Mika Takardan Shiga Gidan Majalissai ga Shamsudeen Dambazau

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC), a ranar Litini da ta wuce ta bayar da Takardan komawa kan kujerar wakilanci a Gidan Majalisar Tarayyar a Jihar Kano ta yankin Sumaila da Takai ga Shamsuddeen Dambazau, ‘da ga Ministan Harkokin Kasa, Abdulrahman Dambazau.

Naija News Hausa na da fahimtar cewa Hukumar INEC a can baya ta bayar da takardan ne ga Kawu Sumaila, Tsohon Ma’aikaci da Mai Wakilcin shugaba Muhammadu Buhari a lamarin gidan Majalisar Dattijai.

Ka tuna a baya da cewa Kotun Koli ta Jihar Kano, a ranar 18 ga watan Afrilu da ya gabata, ta cire Mista Sumaila  daga matsayin wakilcin Jihar Kano a Gidan Majalissai, a karkashin Jam’iyyar APC.

Kotun tayi hakan ne bisa zargi da kara da Dambazau ya gabatar a gaban Kotun Koli da cewa Kawu-Sumaila bai dace da matsayin ba don bai shiga tseren takaran Firamare da aka yi a Jihar Kano ba, kamin zaben Tarayya da aka yi.

A ranar Litini, 13 ga watan Mayu da ta wuce, Amina Zakari, Kwamishanan Hukumar INEC ta Tarayya ta bayar da takardan komawa ga kujerar gidan Majalisa ga Dambazau, ta kuma bayyana da yin hakan ne bisa umarni da dokar kotu.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi barazanar cewa zai barranta kujerar Mulki shugaban kasa, Idan Kotun Kara ta gabatar da Atiku da cin zaben shugaban kasa ta shekarar 2019 da aka kamala a baya.

Ko da shike Shugabancin kasa ta gabatar da cewa za a rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu ta 2019.