Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 15 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 15 ga Watan Mayu, 2019

1. Majalisar Dattijai ta kafa binciken kan zaben Emefiele da Buhari yayi

A ranar Talata da ta wuce, Gidan Majalisar Dattijai sun fara kadamar da binciken Godwin Emefiele, da dalilin da yasa shugaba Buhari ya sake nada shi Gwamnan Bankin Tarayyar kasar Najeriya ta karo biyu.

Wannan matakin Majalisar ya kafu ne bayan da jagoran Majalisar, Ahmed Lawan yayi kiran kulawa da lamarin da kuma hadin kan Sanata Philip Aduda, a jagorancin shugaban gidan Majalisar, Sanata Bukola Saraki.

2. Bukata na Inje Karatu Kasar Waje, inji Yaron da Ya ci 347 a JAMB

Ekene Franklin, Dan Yaron da ya fiye kowa ga Jarabawan JAMB ta shekarar 2019, wada aka kamala makonnan da ta gabata ya bayyana da cewa baya son nasarar shi ta zama a banza.

Ekene dan shekara 15 ne kawai ga haifuwa kuma ya nada muradin shiga UNILAG, amma doka ta hana hakan bisa tsawon shekarun sa. Sai dai Ekene bai raunana ga zuciyarsa ba.

3. Ina da bugun gaban cin nasara ga zama Kakakin gidan Majalisa – Gbajabiamila

Dan takaran kujerar zama Kakakin yada yawun gidan Majalisar Dattijai daga Jam’iyyar APC, Femi Gbajabiamila, ya bayyana da cewa yana da tabbacin cewa zai lashe kujerar tseren kakakin gidan majalisa.

Mista Femi ya bayyana hakan ne a ranar Talata da ta gabata, a birnin Abuja daga bakin jagoran kungiyar hidimar neman zaben Gbajabiamila ga kujerar kakakin gidan majalisa, Mista Abdulmumin Jibrin.

4. Jihar Kwara: Karya ake da zancen cewa na mika Takardan WAEC mara kyau ga INEC – inji Abdulrazaq

Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq yayi murabus da zancen da ake na cewar ya bayar da takardan WAEC mara kyau ga Hukumar gudanar da zaben kasar (INEC), a zaben 2019 da aka kamala.

Alkalin da ke wakilcin Abdulrazaq a kotu, Mista Lawal Jimoh ya bayyana a yau ga Kotun Koli ta Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, cewa Gwamna Abdulrazaq ya kamala karatun sakandirin shi ne a Government College ta Kaduna a watan Yuli ta shekarar 1976.

5. Abin da Kotun Karan Zabe ta fadi game da nasarar Shugaba Buhari a zaben 2019

Kotun Karan Zaben ta birnin Abuja ta gabatar da daga ranar gudanar da karar nasarar shugaba Muhammadu Buhari ga zaben ranar 23 ga watan Fabrairun da aka kamala.

Naija News Hausa ta tunar da cewa Jam’iyyar HDP (Hope Democratic Party – HDP) ta bukaci cewa a dakatar da rantsarwa da ake batun yi ga shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 ga Watan Mayu 2019.

6. Kungiyar ‘Yan Biafra: IPOB sun gabatar da ranar Tunawa da ‘Yan Kungiyar su da aka kashe

Kungiyar ‘Yan Iyamiran Najeriya da ke yaki da neman yancin Biafra, IPOB sun dage da cewa zasu katange rukunonin kasar Biafra a ranar 30 ga watan Mayu don tunawa da ‘yan kungiyar su da aka kashe a shekarun baya.

“Zamu bayyana ga ‘yan kasar Biafra duka da kuma Al’ummar Najeriya gaba daya da cewa kungiyar IPOB ce kawai hadaddiyar kungiya da ke yaki ta kwarai da neman yanci a ko ta ina” inji bayanin kakakin yada yawun kungiyar IPOB, Emma Powerful, a ranar Litini da ta gabata.

7. Gwamnatin Tarayya zata kafa Kwamitin Biyan Kankanin Kudin Ma’aikata

Gwamnatin Tarayyar kasar Najeriya na kokarin kafa Kwamitin da zasu kadamar da biyan kankanin kudin ma’aikata na naira dubu N30,000 da aka amince da ita a baya, a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News Hausa ta gane da cewa Kwamitin zai shafi hadewar Ministoci 7 hade da shugaban harkokin Ma’aikatanĀ  Tarayya, Malama Winifred Oyo-Ita, a matsayin Ciyaman na Kwamitin.

8. Ribadu ya Wakilci shugaba Buhari a zaman Kotun Karar Zabe

Mista Nuhu Ribadu, Shugaban Gabatarwar Hukumar EFCC, a ranar Talata da ta gabata ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari a zaman Kotun Karar Zabe.

Naija News ta fahimta da cewa Ribadu ya wakilci Buhari ne a karar da Jam’iyyar HDP da dan takaran su, Ambrose Awuru ya gabatar na cewar a dakatar da hidimar rantsar da shugaba Buhari.

9. Karya ne, ban janye daga Jam’iyyar PDP zuwa APC ba – Ortom

Gwamnan Jihar Benue, Mista Samuel Ortom, ya gabatar da rashin amincewa da jita-jita da ake yi da cewa yana da shirin janyewa daga Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) zuwa Jam’iyyar shugabancin Kasa, APC.

Ortom ya bayyana hakan ne a wata sanarwa ta bakin kakakin yada yawun sa, Terver Akase, da cewa Gwamnan ya dai bayyana ne da cewa yana jin dadin muhawar da zamantakewar shi da shugabannan Jam’iyyar APC a Jihar Benue da Tarayyar Kasar.

Ka samu kari da cikakken labarun Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com