Kannywood: Takaitaccen Labarin Umar M. Sharif, Shahararren Mawaki

Umar Muhammadu Sharif yana daya daga cikin Shahararrun mawaƙan hausa masu mahimmancin kwarari da gaske.

Sharif ba Mawaki ne kawai ba, Dan kasuwanci a fagen wasa, yana kuma da kyautannai lambar yabo mai yawa da ya karba a fagen shiri.

An haifi Sharif ne a shekarar 1987, ya kuma yi karatun Makarantar Firamare da Sakandiri ne a garin su, Rigasa ta Jihar Kaduna.

Umar ya bayyana da cewa shi ya kasance ne dalibi mai mahimmanci kuma tun lokacin yarantakarsa, abin da ya sa shi cikin raira waƙa shi ne wani abin da ya faru tsakanin shi da ƙaunarsa na farko, kamar yadda ya fada wa BBCHausa.

“A da ni dalibi ne na kwaran gaske, kuma tun a baya lokacin da nake makarantar sakandiri, ni Musulmi ne na gaske.”

YADDA M. SHARIF YA SHIGA FAGEN WAKA

Umar M. Sharif ya bayyana a wata ganawa da manema labaran BBC Hausa da cewa lallai ya shiga fagen Waka ne sakamakon wata abun da ya gudana tsakanin shi da yarinyar da yake soyayya da ita a da.

Ya Bayyana a haka;

A wata ranar haka a lokacin da nake dan matashi na, akwai wata kyakyawar yarinya da nake so kwarai da gaske a kauyan mu, amma don rashin kwarewa na da soyayya da kuma zamancewar fadawa ga soyayya a karo ta farko, kunya ya cika ni kwarai da gaske har na kasa bayyana a gaban ta in gabatar da so na.

Bayan da na gayawa abokan arziki, sai suka shawarce ni da isa har ga kofar gidan su da kuma kiran ta, ni ko sai na kokarta da yin hakan.

Amma abin takaici, duk lokacin da na aika da kiranta, idan na ji motsin ta da fitowa sai in labe ina leken ta daga nesa don tsoron fuskantar ta ido-da-ido. Ita kuma idan ta fito, sai ta juya hagu da dama, idan kuma bata gan mai kiran ta ba sai ta koma cikin gida, a lokacin ni kuma ina boye da leken ta, Na yi hakan ne har kusan sau Uku.

A rana guda kwaram sai na kudurta cewa ba zani kara boyewa ba idan ta fito. Na kakkabe takalma na sai na hari gidan su, Ina isa a gaban gidan sai na aika mata, amma abin takaici a gareni, yarinyar taki fitowa a ranar.

Wannan ya zafeni kwarai da gaske, da bari na da mammakin dalilin da ya sa ta ki fitowa. Ganin hakan sai na kafa baki ga wakewake don lafar da zafin zuciya na, na kuma kama hanyar gidan mu. 

A duk lokacin da na tuna da al’amarin, sai in kafa baki ga wakewake. Na ci gaba da yin hakan har sai da wani Yaya na da ke zaman Mawaki ya ji ni. 

Da kuma ya gane da zakin murya na da kwarewa na, sai ya dinga bani shawarwari akan yadda zan kara kwarewa ga wakewake. Bayan ‘yan lokatai kuma, sai ya tallafa mani ga yin rikodi na ta farko a lokacin.

Wannan ita ce bayanin M. Sharif a ganawar shi da manema labaran BBC a kwanakin baya.

KARANTA WANNAN KUMA; Ba ni aka wa Duka ba, Bata mani suna kawai ake kokarin yi – Inji Bilkisi Shema

A halin yanzu, bisa ganewar Naija News Hausa, Umar M Sharif na da rikodin wakoki kimanin 500 da ya rigaya buga. A cikin hakan aka samu su; Duniya Ce, Nadiya, Madubi, Jinin jikina, Mai atamfa, Bakandamiya, Babbar yarinya da dai sauran su.

Sharif na da kwarewa kuma a shafin fita shirin fim, zaman Furoduza a fagen Kannywood, Ya kuma fito ga Fina-Finai kamar su; Mahaifiyata, Nas, Jinin jikina, Ba zan barki ba, ka so a so ka, dadai sauran su.