Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 16 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 16 ga Watan Mayu, 2019
1. Shugaba Muhammadu Buhari yayi tafiyar Umrah zuwa kasar Saudi Arabia
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi gayyatar Sarki Salman Bin Abdulaziz, da ke jagorancin Saudi Arabia da kuma wakilcin Manyan Masallacin Saudi Arabia biyu, don kadamar da hidimar Umrah a kasar.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa sanarwan da Bashir Ahmed, mai wakilcin shugaba Buhari wajen sadarwa ya bayar a ranar a yau Alhamis, 16 da Watan Mayu.
2. Yadda Manyan ‘Yan Siyasa ke Kadamar da Karfafa Ta’addanci da Kashe-kashen rayuka a Najeriya – Burutai
Babban Ofisa, Shugaba Rundunar Sojojin Najeriya, Lt. Gen. Tukur Buratai ya bayyana a yau bacin ransa ga ta’addanci da kashe-kashen rayuka da ake yi a kasar Najeriya a koyaushe, duk da kokari da rundunar Sojojin ke yi.
Ya kara da zargin cewa ta’addanci a kasar na karuwa ne da taimakon ‘yan siyasa da suka fadi ga zaben tarrayar da aka yi a kasar a baya, “Rundunar Sojojin na da shaida ga wannan zargi” inji shi.
3. Atiku/Buhari: Gwamnatin Tarayya ta gabatar da Gargadi ga ‘yan Jam’iyyar PDP
Gwamnatin Tarayyar Najeriya, a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, na kalubalantan ‘yan Jam’iyyar Dimokradiyya da yin kuwa bayan yaki.
Gwamnatin Tarayyar, a ganewar Naija News, sun bayyana hakan ne da zargin cewa hidima da kadamarwan da Jam’iyyar PDP ke yi na iya jawo tashin hankali a kasar da kuma raunana Dimokradiyyar kasar Najeriya.
4. Rashin Hankali na ya jawo ci gaba ta musanman a Jihar Imo – inji Okorocha
Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Mista Rochas Okorocha, a ranar Laraba da ta wuce ya bayyana kansa da zaman “mara hankali”.
Ya bayyana cewa duk da rashin hankalin sa, hakan ya jawo ci gaba a Jihar Imo bisa ga yadda ya cinma Jihar kamin shigar sa a zaman Gwamna.
5. Kotun Karar Zaben ta gargadi Atiku Abubakar a yadda zai Ci Nasara a Karar Kotu
Kotun Kadamar da Karar Zabe ta birnin Tarayyar kasar, Abuja, ta gargadi Atiku Abubakar, dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, cewa ya wallafa wasikar bukatan Kotun Neman Yanci da da Ciyaman na Kotun, Zainab Bulkachuwa, da janyewa daga karar.
Kotun ta gabatar da gargadin ne ga Atiku a ranar Laraba da ta wuce.
6. Kotun Koli ta Jihar Kano ta Tsige Sarakai Hudu da Ganduje ya Nada
A ranar Laraba, 15 ga watan Mayu da ta gabata, Kotun Koli ta Kano ta sanar da tsige sabbin Sarakai Hudu da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya nada makon da ta gabata.
Mun ruwaito a shafin labarai a Naija News Hausa a baya cewa Masu Nadin Sarauta a Jihar Kanosun gabatar da Lauyoyi 17 don Kalubalantar Ganduje da Kara Kujerar Sarauta Hudu a Jihar Kano.
7. Ku Shirya da marabtan Tsadar Man Fetur, Rewane ya gayawa ‘yan Najeriya
Bismarck Rewane, Babban Ofisan Kadamarwa ga Kamfanoni, ya gargadi al’ummar Najeriya da zama a shirye don karuwa ga tsadar Man Fetur.
Rewane ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da yayi a birnin Legas da cewa za a samu karuwa ga tsadar kudin Man Fetur.
8. HISBAH sun kame Mutane 80 da Cin Abinci a Fili a yayin da ake cikin Azumi
Hukumar Shari’ar Musulunci (HISBAH) ta Jihar Kano sun gabatar da kame mutane 80 a Jihar da zargin cin abinci a Fili, a yayin dan sauran ‘yan uwa Musulumai ke cikin Azumin Ramadan.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Jihar Kano na daya daga cikin Jihohin Najeriya da ke amfani da Shari’a Musulunci kwarai da gaske, musanman tun shekarar 2000.
Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com