Connect with us

Uncategorized

#Ramadan: HISBAH sun kame Mutane 80 da Cin Abinci a Fili a yayin da ake cikin Azumi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Shari’ar Musulunci (HISBAH) ta Jihar Kano sun gabatar da kame mutane 80 a Jihar da zargin cin abinci a Fili, a yayin dan sauran ‘yan uwa Musulumai ke cikin Azumin Ramadan.

‘Yan Hukumar HISBAH sun bayyana cewa lallai sun kame mutanen ne a yankunonin Jihar Kano cikin ‘yan kwanakin da aka fara Azumin Ramadan.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Jihar Kano na daya daga cikin Jihohin Najeriya da ke amfani da Shari’a Musulunci kwarai da gaske, musanman tun shekarar 2000.

Ka tuna a baya cewa Naija News Hausa ta ruwaito da cewa ‘Yan Kungiyar HISBAH ta Jihar Kano sun yi alkawarin kama duk wani Musulmi wanda ya kauracewa yin azumin watan Ramadan.

Bisa bayanin kakakin yada yawun HISBAH na Jihar Kano, Adamu Yahaya, ya bayyana ga manema labaran BBC da cewa Musulumai ne dukan mutane Tamanin da hukumar su ta kama, “HISBAH ba sa kamun wadanda ba Musulumai ba don dokar Islam ba ya a kansu” inji shi.

“Daga cikin mutanen da muka kame, sun bayyana cewa sun ci abinci ne don basu ga fitar watan Ramadan ba da kansu, sauran mutanen kuma sun bayyana da cewa sun ci abinci ne don basu da lafiyar jiki”

“Hukumar ta gane da cewa bayanan su bai da wata manufar kwarai, kuma ba abin diba bane. Amma dai an gargade su, an kuma sake su da diban cewa karo ta farko ke nan da suka karya doka” inji Malam Yahaya.

Malam Yahaya ya kara da cewa sun gargadi mutanen da bin dokar, akan cewa idan aka kara gane su da cin abinci a yayin da azumi ke gudana, lallai zasu kame su, a kuma kai ga Kotu.

“Azumin Ramadani dole ne ga dukan ‘yan uwa Musulumai, sai dai kawa ba dole ba ga wadanda ke cikin yanayin rashin lafiyar jiki” Yahaya.

Ya karshe da cewa HISBAH za ta ci gaba da kadamar da bincike a yayin da ake cikin Azumin, don kame duk wanda ya kaurace wa dokar.

KARANTA WANNAN KUMA; Hukuma ta jefa wani mutum mai suna Sani Ibrahim a kurkuku a Jihar Katsina sakamakon zargin yi wa wata ‘yar shekaru bakwai, diyar makwabcin sa fyade.