Connect with us

Uncategorized

Boko Haram: Yadda aka Bizine Sojojin da suka Mutu a Filin Yaki ta ranar 13 ga watan Mayu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya ta gudanar da hidimar zana’izar Sojojin kasar da suka mutu a wata ganawar wuta da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Mauli-Borgozo, a ranar Litini, 13 ga watan Mayu da ta gabata.

Mutuwar Sojojin ya faru ne a yayin da suke zagayen yaki da ‘yan ta’adda a yankunan Jihar Borno.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Marigayi Lieutenant Colonel Yusuf Ibrahim Aminu ne Babban Ofisa da ke wakilcin Rundunar Sojojin ‘154 Task Force Battalion Borgozo’. Yana cikin jagorancin dakarun yakin ne a yankin Mauli- Borgozo, a yayin da motar shi ta fada ga wata Bam da ‘yan ta’addan suka haka, Bam din ta kuma tashi da Motar tare da shi da sojoji biyu da ke a cikin motar.

A hakan ne Babban Jami’in Rundunar Sojojin Najeriya ta Tarayya, Lt Gen, Tukur Buratai, ya jinjina wa kokari da gwagwarmayan rukunin rundunar sojojin ta Operation Lafiya Dole, da mazantakar su wajen fuskantar ‘yan ta’adda a kasar Najeriya.

“Ko da shike mutuwar darukan yakin ya zafe mu kwarai da gaske, amma wannan ba zai raunana mu ba, sai dai kara karfafa sauran sojoji wajen kadamar da ayukan su na tsaro da yaki da ta’addanci a kasar” inji Buratai.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Rukunin Rundunar Sojojin Najeriya ta Operation LAFIYA DOLE sun gabatar da ribato mata 29 hade da ‘yan yara 25 a wata kangin ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a Jihar Borno.