Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Kotun Majistare ta bada Umarnin kame Hadiza Gabon

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Babban kotun majistare ta Jihar Kano ta bada umarnin kame ‘yar shirin fim a Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon.

Ka tuna cewa Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shahararriyar ‘yar shirin fim a Kannywood, Amina Amal ta wallafa kara ga Kotu Koli ta Jihar Kano, a kan fadan ta da Hadiza Aliyu Gabon.

Amal ta gabatar da cewa Hadiza ta ci mutuncin ta da kuma muzurta ta, a hakan ne ta wallafa kara da bukatar Kotun Koli ta Jihar Kano da tsananta da kuma sa Hadiza ta roke ta da kuma biyar ta kudi kimanin naira Miliyan Hamsin (N50m) hade da manyan shaidu biyu a gaban kotun.

Naija News Hausa ta samu fahimtar cewa Kotun Koli ta bada umarnin gaugawa ne ga kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Mohammed Wakili da kame Hadiza.

Kotun ta gabatar da hakan ne don kauracewar da Hadiza ta yi ga kirar da Kotu ta yi a gareta. An bayyana da cewa Kotun ta gayyaci Hadiza Gabon a baya da halarta a gaban kotun don bayani bisa wata zargi da Mustapha Badamasi Naburaska ya gabatar ga kotun.

Babban alkalin kotun, Muntari Dandago ya bada umarnin kame Hadiza ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

Alkalin ya kuma bukaci ‘yan sanda da kara kadamar da bincike don samun tabbacin ko gaskiya ne zargin da aka yi ga Hadiza.

KARANTA WANNAN; Takaitaccen Labarin Umar M. Sharif, Shahararren Mawaki a Kannywood