Connect with us

Uncategorized

#Ramadan: Hukumar INEC ta daga ranar zaben Gwamnonin ta Jihar Kogi da Bayelsa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC), ta gabatar da daga  ranar yin zaben Gwamnoni ta Jihar Kogi da Jihar Bayelsa zuwa gaba.

Naija News Hausa ta fahimta cewa Hukumar a farko ta sanar da kadamar da hidimar zaben ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, amma a yanzu za a yi hakan ne a ranar 16 ga Nuwamba.

Hukumar INEC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da darektan INEC wajen samar da ilimi ga masu jefa kuri’a, Mista Festus Okoye, ya bayar a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

Wasu masu ruwa da tsaki daga Jihar Bayelsa sun bukaci hukumar INEC da su canza ranar zaben a yayin da ranar da aka sanya ga zaben ya kasance rana daya da ‘Ranar hidimar nuna godiyan’ Jihar da suka saba wadda ke bisa dokar Jihar.

Mista Festus ya ce, “Bayan binciken da aka yi a kan shari’a da dokar hukumar, Hukumar ta gudanar da taro na mako-mako da ta saba yi a yau, 16 ga watan Mayu, anan ne kuma ta yanke shawara da daga ranar zabukan gwamnonin a Kogi da Bayelsa zuwa ranar Asabar 16 ga Nuwamba 2019”

KARANTA WANNAN KUMA; Kotu ta Mika Takardan kujerar wakilci a Gidan Majalissai ta Jihar Kano ga Shamsudeen Dambazau,