Connect with us

Uncategorized

Farmaki ya tashi a Kaduna a yayin da ‘Yan Sandan suka Kashe wani Mazaunin Sabon Kawo da Bindiga

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mazauna Jihar Kaduna sun kai hari a babban hanyar Kaduna-Zaria da Kaduna-Lagos, sun katange manyan hanyoyin da kone-konen tayoyi da wuta don nuna rashin amincewar kisan wani da ‘yan sanda suka yi.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa rikicin ya barke ne bayan da mazauna garin Kawo a safiyar yau Litinin, 20 ga watan Mayu, suka karbi bayani cewa wasu masu sace-sacen mutane kimanin uku na kokarin sace mutanen unguwar.

Bisa bayanin daya daga cikin mazaunan shiyar, ya bayyana ga manema labarai cewa anan take ne mutanen anguwar suka tare manyan hanyoyin da ta shiga garin, suka kuma hari masu sace-sacen mutanen har ma sun samu kame daya daga cikin su, daga nan kuma suka haska masa wuta nan take.

Suna cikin hakan ne jami’an tsaro ‘yan sandan yankin suka samu labarin hakan, kwaram sai suka hari kauyan don sauya matakin mazaunan kauyan, a garin harbe-harbe ‘yan sandan a iska sai harsasun bindiga ya tabi mutanen kauyan, harma wani ya mutu sakamakon hakan, wasu kuma suka yi raunuka.

“Na hango jama’a ne makil a kauyan da hayaniya daga nesa. Mutanen Kawo da jin labarin cewa masu sace-sacen mutane na cikin Sabon Kawo sai suka tari hanyoyin garin duka”

“Sun hari mutanen a nan take kuma suka kashe mutum guda daga cikin su. A isowar Jami’an tsaro kuma sai suka fara harbe-harbe a iska don korar mutane, daga nan harsasun bindiga kuma ya tabi mutane har ma mutum daya ya mutu a nan wajen”

“Mutane hudu harsashen ‘yan sandan ya sama, mutun guda ya mutu daga cikin su, sauran ukkun kuma suna a Asibin Janara wajen kulawa” inji Sadi Dauda, Mazaunin Sabon Kawo da ya samu ganawa da lamarin.

Ya kara da cewa mazaunan Sabon Kawo sun mamaye Ofishin Jami’an tsaron da neman su saki barawon da ke a Ofishin su don su yi abin da ya dace da shi.

“Sun ce ba zasu bar Ofishin Jami’an tsaron ba sai har sun saki barawo gudan” inji Dauda.