Connect with us

Uncategorized

Jami’an Tsaro sun Kame Wani Sojan Karya a birnin Legas

Published

on

at

advertisement

Wata rukunin ‘Yan Sandan Najeriya (Rapid Response Squad -RRS), ta Jihar Legas sun kama wani Sojan Karya a Legas, sanye da Kakin Sojoji.

An kama matashin ne mai suna Yusuf Quadri a Mobolaji Bank Anthony, hanyar da ta bi kusa da filin jirgin saman ta Muritala Muhammed a Legas.

Bisa ganewar manema labarai, Ofisoshin RRS sun kame Quadri ne a lokacin da suke kan hanyan bincike.

“Quadri ya bayyana kansa a matsayin Sojan Najeriya ne a lokacin da aka tare shi. Amma da Jami’an tsaro suka lura da kuma tugume shi da kyau, sai aka gane da cewa Sojan karya” inji Manema labarai da suka karbi rahoton.

Bayan bincike, an iya gane cewa karatun Firamare ne kawai Quadri yayi.

Ya kuma bayyana ga Jami’an tsaro cewa lallai ya sace Kakin wani Ofisan Soja ne da ya taimaka wa da daukan kaya.

“Na sace kakin ne a daga wani Soja da aka kara wa igiya, na kuma yi hakan ne a lokacin da nike taimaka masa da daukar kayan sa. Daga nan kuma sai na dauki hoto da rigar na shigar da shi cikin fasfot, na kuma ci gaba da amfani da kakin don aikata mugun hali”. inji Quadri.

Ya karshe da cewa yakan yi amfani da Kakin da Fasfot din ne idan yana son ya samu yancin fita a duk wata hanya da Jami’an tsaro ko Hukumar LASTMA suka tare.

A halin yanzu an riga an karbi rigar daga hannun sa hade da fasfot din, ko da shike ba a bayyana yadda aka karshe da shi ba, amma akwai sanin cewa yana dakile a hannun Jami’an tsaro.

KARANTA WANNAN KUMA; Wani Mutum mai Shekaru 40 yayi wa ‘yar Shekara 7 Fyade a Kano