Kalli Yada wani Soja ya wa wani Shahararren Mawaki a Najeriya Duka

Wani shahararren mawaki, dan Najeriya mai suna, Friday Igwe da aka fi sani da suna Baba Fryo, ya bayyana yadda wasu Sojojin Najeriya da ba a san da su ba suka yi masa duka a birnin Legas.

Fryo tsohon mawaki ne a Najeriya tun shekaru 1990s da suka gabata. An fi sanin shi da wata waka mai liki “Denge Pose”, Idan kana tsarar wannan shekarun ko fiye da haka, zaka gane Fryo da kyau.

Fryo ya rabar da hoton sa a layin yanar gizon da yadda sojojin suka bata masa fuska da bugu, ko da shike dai bai bayyana sanadiyar hakan ba, amma da alaman an zalunce shi.


“Wasu Sojoji da ba a san da su ba sun zalunce ni, sun kuma ci mani mutumci, na yi kokarin in ja su zuwa Bariki, amma ‘yar macce da ke cikin su ta kafa baki ga zancen, ta kuma sa mazan sun gudu”

“Na gode ga Barikin Sojojin da ke a Ojo ta birnin Legas, da yadda suka kafa baki ga lamarin, ina fatan Allah ya basu nasara ga kame wadanda suka yi mini wannan irin bugun, a kuma dauki mataki da ya dace da su” inji Baba Fryo.

KARANTA WANNAN KUMA; HISBAH sun kame Mutane 80 da Cin Abinci a Fili a yayin da ake cikin Azumi