Connect with us

Uncategorized

HISBAH sun kame Karuwai 21 da Fashe Kwalaban kayan Maye a Jigawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Jigawa, HISBAH, a ranar Litinin ta kama mutane 21 da ake tuhuma da aikata laifuka da bai dace ba, haka kazalika suka kwashe wasu kwalabai kimanin 111 daga hannun su.

Babban kwamandan Hisba a jihar, Ibrahim Dahiru, wanda ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na NAN a Dutse, ya bayyana cewa sun kame mutanen ne a karamar hukumar Kazaure na jihar Jigawa.

Dahiru ya bayyana cewa hukumar sun kadamar da zagayen ne a safiyar ranar Litini a sanannen haɗin hanyar Gadar Kazaure.

Ya bayyana cewa, a yayin harin zagayen, sun kame mutane 14 da ake zargi da aikin Karuwanci hade da maza bakwai.

Kwamandan ya yi zargin cewa an kama su ne da laifin aikata ayyukan lalata a Jihar, da cewa kuma an riga an gabatar da su a Kotun Sharia’a ta Kazaure.

“HISBAH zata ci gaba da yaki da halin Lalata da shaye-shayen kayan Maye a Kasar’ inji Dahiru.

Ya gargadi al’ummar Jihar da janye daga irin wadannan halayen, “Irin wadannan halayen zai iya lallatar da yanki da kuma kasar mu” inji shi.