Uncategorized
Mugunta! Wani ya yanke maƙogwaron abokinsa don neman sace Masa Babur
Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa Jami’an tsaron Jihar Jigawa sun kame wani mutum mai suna Sale Shanono, mazaunin Doguwa, a karamar hukumar Jahun da laifin yanke maƙogwaron abokinsa.
Gidan labaran nan ta mu ta samu tabbacin labarin kame dan shekara Talatin ne bisa bayanin da kakakin yada yawun Jami’an tsaron yankin, SP Abdu Jinjiri ya bayar.
SP Jinjiri ya bayyana da cewa ‘yan sanda sun karbi rahoto a ranar Litinin a kimanin karfe takwas na dare da cewa wani mutum da ake kira da suna Yakubu Amadu na karamar hukumar Dogawa Jahun ya dauki abokinsa a kan babur don ya tafi tare da shi zuwa gidan surukansa don taimaka masa wajen rokon matarsa.
Bisa bayanin Jinjiri, A isar su wata dogon daji sai abokinsa, Sale Shanono yayi amfani da wuka daga baya ya yanke abokinsa a wuya, ya kuma yi wuf da daukar Babur dinsa ya gudu.
Ko da shike Yakubu bai Mutu ba, amma ya yi zubar jini da rauni kwarai da gaske.
“Sale a ganin sa, Yakubu ya riga ya mutu ba tare da sanin cewa bai mutu ba tukunnan” inji SP Jinjiri.
“A isar Jami’an tsaro a wajen bayan ganewa da hakan, sai aka yi gaggawa da kai Yakubu a Asibiti don bashi kulawa a babban Asibitin Jahun”
Ya karshe da cewa lallai an nemi Sale and kuma kame shi, aka kuma kwace babur din daga hannun sa.
A halin yanzu ana kan bincike game da al’amarin kamin a kai shi a Kotu.
KARANTA WANNAN KUMA; So ta kai wani Fulani ga Mutuwa a Filin Sharo