Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben2019: Atiku zai ci Nasara da Buhari a Kotu – PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jam’iyyar PDP a ranar Litinin, 20 ga Mayu, sun sake buga gaba da bada gaskiya da cewa dan takarar shugaban kasa na shekarar 2019 a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubabar zai ci nasara ga karar shugabanci kasar Najeriya da ake a Kotun Zabe.

Jam’iyyar adawan sun yi kira ga kwamitin karar da tabbatar da cewa an gudanar da karar a yadda ta dace da kuma adalci.

Naija News Hausa ta fahimta a bayanin Kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP na Tarayya, Mista Kola Ologbondiyan cewa Shugaban kasar, Buhari ya kasa a sassa uku da kasar ke begen shi da ita tun daga shekarar 2015.

A cikin jawabinsa, PDP ta kara da cewa Jam’iyyar APC ta ci gaba da raunana shugabannin PDP da kuma gabatar da zarge-zarge kan dan takarar su, Alhaji Atiku Abubakar, don jan hankalinsu daga karar da ke gaban Kotu.

“Al’ummar Najeriya sun gane da cewa zamantakewar su a kasar shekarun baya da PDP ke shugabanci yafi dacewa da ta shugabancin Jam’iyyar APC da ake ciki yanzu. Ganin hakan ne muka tunawa al’ummar kasar da hakan, da kuma yin alkawarin tabbatar da cin nasara da halin Talauci, Rashin Tsaro, Cin Hanci da Rashawa da Ta’addanci a kasar” inji Kola.

“Muna da tabbataciyar shaidodi da ya bayyana dan takaran mu da nasara ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019″

A hakan ne Jam’iyyar PDP suka bukaci Alkali Zainab Bulkachuwa da janyewa daga zancen karar don dangantakar ta da shugaba Muhammadu Buhari da kuma Jam’iyyar APC.