Connect with us

Labaran Najeriya

Kotun Karar Zabe ta Gargadi Balkachuwa da Janyewa daga Karar Atiku da Buhari

Published

on

at

Mista Lateef Fagbemi (SAN), lauya ga Jam’iyyar APC a karar shugaban kasa, ya bukaci shugaban kotun daukaka kara, Alkali Zainab Bulkachuwa ya janye daga zancen karar.

Fagbemi, ya bayyana da cewa ko da shike zancen Jam’iyyar PDP da dan takaran su ga zaben shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya kasance mara muhinmanci, amma dai ya shawarci alkalin da yin watsi da hidimar shari’a kan sakamakon zaben ga wanda ya lashe zaben 2019.

Ka tuna a baya mun sanar a Naija News Hausa da cewa Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar sun bukaci Alkali Bulkachuwa da janye wa daga zancen karar, akan cewa tana da liki da Jam’iyyar APC, musanman shugaba Muhammadu Buhari.

Da cewa Bulkachuwa zata iya kadamar da makirci a karar zaben don dangantakarta da Jam’iyyar APC.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wata gargadi mai karfin gaske ga Shahararrun ‘yan wasan Kwaikwayo da Ban Dariya na Najeriya, cewa su janye daga yi masa ba’a wajen hidimar su.

“Ku bar yin ba’a da ni, sauran kasashen waje na da tasu matsalar da suke fuskanta a kasar su. Amma ba zaku taba gan suna yin ba’a ga shugabanan su ba” inji Buhari.Advertisement
close button