Labaran Najeriya
Sabuwar Harin ‘Yan Hari da Makami ya tafi da akalla rayuka 34 a Jihar Katsina
Mahara da Bindiga sun kashe mutane 34 a kauyuka a ranar 21 ga Mayu, a kananan hukumomi uku na Batsari, Dan Musa da Faskari a jihar Katsina.
Bisa bayanin da mazauna yankin suka bayar ga manema labarai, akalla mutane 18 ne aka kashe a yankin Batsari, an kashe mutane biyar a Dan Musa, aka kuma kashe 11 a karamar hukumar Faskari.
An bayyana cewa mutane da daman sun samu raunuka a harin, wasu kuma har yanzu ba a gane da inda suka fada ba da gudun hijira.
SP Gambo Isah, kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar ya bayyana cewa mambobin ‘yan banga aka kashe a Faskari.
A bayanin Mista Gambo, Ya ce “Bisa harin da aka kai a Faskari, wasu mambobin wata kungiyar ‘yan banga na ‘Yansakai daga kauyan Sabon Layi sun hari maharan a cikin dogon daji tun ranar jiya, ba a gan dawowar su ba. A baya aka gane da gawar mutum biyu daga cikin su, mutanen kauyan sun kuma bizine su. A wata zagayar bincike da DPO na Faskari ya jagoranta, su ma sun gano gawaki uku a cikin dajin”
“A halin yanzu Jami’an tsaro na kan kara bincike da neman maharan da kuma ribato rayukan sauran mutane da ba a gani ba” inji Gambo.
A halin yanzu mazauna jihar sun shiga tituna a ranar jiya don gudanar da zanga-zanga da buƙatar gwamnatin Jihar da yin sauri don akan magance rashin tsaro wanda ya rinjaye jihar.”
Ka tuna cewa a bara, gwamnan jihar, Aminu Masari, yayi kiran kai tsaye cewa jihar na cikin katangewar ‘yan hari da makami da ‘yan ta’adda.
Haka kazalika a watan Afrilu da ta gabata, ‘yan hari da bindiga suka sace mahaifin matar wani babban jami’in tsaron Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke zama a Daura, ƙauyen Shugaba Buhari.