Connect with us

Uncategorized

Ta’addanci: ‘Yan Hari da Makami sun kashe a kall mutane 17 a Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Hari da Makami run kai wata sabuwar hari a Jihar Zamfara da kashe mutane akalla 17

Naija News Hausa ta karbi rahoton sabuwar harin ‘yan hari da bindiga a kauyuka uku na karamar hukumar Birnin Magaji, Jihar Zamfara. inda suka kashe akalla mutane 17.

Mazauna sun bayyana ga manema labarai da cewa maharan sun kai harin farkon ne a Gidan Kaso a ranar Asabar da ta gabata, suka kashe akalla mutane bakwai.

“Maharan sun hana mazaunan kauyan da daukar gawakin mutanen da suka kashe sai har da hukumomin tsaron yankin suka isa wajen” inji bayanin Tukur.

Tukur Yusuf, ya bayyana cewa wasu ‘yan hari kuma a ranar Lahadi sun kai hari a kauyan Dan Dambo, inda suka kara kashe mutane hudu da kuma sace masu dabbobin su.

“Haka kazalika suka kara kashe mutane bakwai daga kauyen Kokeya da suka iso wajen taimaka wa mutanen kauyukan da aka fara kai hari, suka harbe su da bindiga.

Ko da shike ba a samu karban rahoto daga kakakin Jami’an tsaron Jihar ba a lokacin da aka bayar da rahoton, amma dai mutanen kauyukan da suka yi gudun hijira sun fara dawo wa don ci gaba da zaman su a kauyukan su.

KARANTA WANNAN KUMA; Aminu Tambuwal, Gwamnan Jihar Sokoto yayi barazanar cewa ba wanda ya isa ya dakatar da hidimar rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Sokoto a ranar 29 ga watan Mayu ta shekarar 2019.

Naija News Hausa ta fahimta cewa Tambuwal yayi wannan furcin ne don ya gane cewa akwai wasu a Jihar da ke kokarin kadamar da tashin hankali da tada tanzoma a Jihar.