Connect with us

Uncategorized

Wani Babban Jami’in Sojan Najeriya ya Kone a Gobarar Hadarin Mota

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani Babban jami’in sojan Najeriya da aka fi sani da suna Major A.N Efam, a ranar Litinin, ya rasa ransa a yayin hatsarin motar da yayi a Ojo, a jihar Legas.

Naija News Hausa ta fahimta cewa hadarin ya faru ne da Jami’in da safiyar ranar Litinin, 20 ga Watan Mayu.

Hakan ya faru ne a yayin da wani babban Jami’in Soja mai suna M.A Tombri ya ke kokarin kaucewa daga kan hanyar rukunin Sojojin, a kan hakan ne Mista Efam ya kafa kai ga hanyar da wata motar Peugeot, ya kuma hade da motar Mista Tombri.

Anan take ne Motar Major Efam ya dauke da gobarar wuta, kamin ya samu taimakon mutanen shiyar ya riga ya kone da wuta kurmus.

Ko da shike Manema labarai sun yi kokarin samun karin bayani game da hadarin, amma dai hakan bai samu ba.

Sai dai an riga an fitar da gangar jikin Meja Efam daga cikin Motar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa gobarar wuta da ya faru a ranar 7 ga Watan Mayu ya tashi kone yara mara sa iyaye da ake bawa kulawa a Jihar Kogi.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, abin ya faru ne a hanyar Agala Ate ta shiyar Aniygba, a Jihar Kogi.