Connect with us

Uncategorized

A haka Al’ummar Katsina cikin hawaye suka bizine mutane 18 da ‘yan Hari suka Kashe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kashe-Kashe a Najeriya: Mahara da Bindiga sun mamaye Jihar Katsina na hare-hare

Cikin kuka da hawaye, anyi zana’izar mutane goma sha takwas da ‘yan hari da makami suka kashe a Jihar Katsina kwanan baya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa ‘yan hari da makami sun kai wata sabuwar hari a kananan hukumomi uku a Jihar Katsina da barin mutane kwance cikin jini.

A wata sanarwa da aka bayar a yau, Naija News ta fahimta cewa an taro gawakin mutanen ne a yankunan da aka kashe su, aka kuma kai su a gidan ajiyar gawa, bayan hakan ne aka gabatar da hidimar bizine su duka.

An yi hidimar addu’ar karshe ne ga gawakin a fadar mai martaba sarkin Katsina, kamin dada aka bizine su.

Babban Limamin Masalacin Jumma’a ta Tsakar Katsina, Malam Mustapha Ahmad ne ya jagoranci hidimar addu’ar.

Haka kazalika hidimar ya samu halartan mutane dari bisa dari daga yankunan don taya su jinya, fatar aljanna da kuma nuna bakin cikin su da rasa ‘yan uwansu ga irin wannan mugun hari na ‘yan ta’adda.

A halin yanzu, mutanen kananan hukumomin Dan Musa da Faskari na cikin bakin ciki da kuka da rasa kimanin mutane 26 ga ‘yan hari da bindiga cikin makonnan da ake a ciki.

KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Sanda da Hukumar NDLEA sun kame Masu sayar da Mugayan Kwayoyi a Adamawa.