Uncategorized
Ka bani karin Wata Uku, Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ya roki Gwamna Abdullahi
A ranar Laraba, 22 ga watan Mayu da ta gabata, Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Gwamna Tanko Al-Makura ya roki sabon Gwamnan Jihar, Abdullahi Sule, da ya lashe zaben 2019 da cewa ya bashi karin tsawon watannai uku don ya gyara Jihar.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Al-Makura ya nemi daman hakan ne ranar Laraba, a nan Ofishin da ake kadamarwar kananan hukumomin Jihar da Nade-naden sarauta.
Anan ne tsohon gwamnan Jihar ya bukaci Gwamna Sule da bashi dama da karin watannai Ukku don ya cika gurin sa ga kai kasar a inda ya dace.
Hakan ya faru ne a yayin da ake hidimar nadin sarauta goma sha shidda a Jihar.
“Saboda irin guri da ganin gaba da nike da shi ga Jihar, shekaru takwas da na yi a jagorancin Jihar bai ishe ni ba; da na samu dama ne daga sabon gwamna, da na ce ya bani karin watannai uku don kamala wata kyakyawar shiri da nike da shi ga Jihar nan” inji Ma-Kaura.
“Ba don da dokar kasa ba zata bada daman hakan ba, lallai da na bukaci karin watannai uku don cika da kuma kamala kyakyawar shiri da nike da shike ga kasar”
A yayin da yake nadin sarakai da wakilai shiddar, ya bayyana cewa lallai hidimar nadin sarautan ya kasance ne da jinkiri don wata matsala hare-hare da kashe-kashen rayuka a Jihar.
Ya kuma karshe da gargadin mutane Jihar da hada kai don ci gaban Jihar. “Duk da cewa akwai matsalar nuna banbanci da kuma zamantakewa a Jihar, Na gargadi alummar Jihar na hada kai da zama tsinsiya daya kuma.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnatin Jihar Filato ta rabar da Kujerar Sarautan Jos, ta cire Arewacin Jos da kuma Sarautan Riyom daga hadaddiyar sarautan Jos da ke a karkashin jagorancin Gbong Gwom na Jos, Yakubu Gyang Buba.