Connect with us

Uncategorized

2019: Kotu ta bada Nasarar Zaben Gwamnan Jihar Zamfara ga Dan takaran PDP

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Jumma’a, 24 ga Watan Mayu 2019, Kotun Koli ta birnin Abuja ta gabatar da tsige dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Zamfara daga Jam’iyyar APC a zaben 2019.

Naija News ta samu sanin cewa Kotun ta yi hakan ne bisa gane da cewa dan takaran na Jam’iyyar APC bai kasance da zaben Firamare ba.

Karar da Alkalan Kotu biyar suka wakilta ya karshe a kan dakatar da dan takaran APC da zargin cewa Jam’iyyar bata kadamar da hidimar zaben Firamare ba a Jihar, kamar yadda aka sanar a shafin labarai a watannan da suka gabata.

Bisa rahoton da aka bayar ga Naija News Hausa a yau, Kotun, a jagorancin Alkali Paul Adamu Galinji, ta gabatar da yin watsi da dukan kuri’un da Jam’iyyar APC ta samu a zaben 2019, an kuma bayyana dan takara na biye da shi ga sakamakon zaben Gwamnoni Jihar a matsayin tabbatacen mai nasara ga zaben.

Alkalin ya kuma gabatar da zargin biyan kudi naira Miliyan Goma N10m ga Jam’iyyar APC.

Kwamitin Kotun ta kuma kalubalanci dukan ‘yan siyasa da janye daga halin raunana dimokradiyyar kasar Najeriya.