Connect with us

Uncategorized

Kalli yada wani mai Turin Baro ya biya wa kansa kudin makaranta har ga kamalawa

Published

on

Duk da mawuyacin halin rashin kudi da abin biyan arziki da ‘yan Najeriya ke fuskanta, hakan bai hana wani matashi cika gurin sa da kuma kai ga hangen sa ba.

Naija News Hausa ta gane da wani dan matashi da ya biya wa kansa kudin makarantar Jami’a babba har ya karshe da kuma shiga Hidimar bautan Kasa (NYSC).

Labarin wannan Matashin ya mamaye ko ta ina a layin yanar gizo, akan irin nuna kuzari da mazantaka da ya nuna don cinma hangen sa.

Bisa bincike da fahimta, gidan labaran na tamu ta samu fahimtar cewa matashin, Aliyu Abbani ya fito ne daga Iyalin da biyan bukata, ci da sha ya zamana da wahala a garesu. Duk da hakan Aliyu bai raunana ga zuciya ba amma ya dauki matakin shiga aikin turin baro, a hakan ne kuma ya dinga biya wa kansa kudin makaranta har ya karshe.

Aliyu ya yi karatun Digiri ne a babban Makarantar Jami’a na Jihar Nasarawa, watau ‘Nasarawa State University. Ko da shike ba a bayyana shashen karatun sa ba, amma dai akwai fahimta da cewa da turin baro ne ya biya wa kansa kudin makarantar har ya gama.

Wannan Kuzari na Aliyu ya zan babban abin Koyi ga Matasa Maza da Mata a kasar Najeriya, musanman wadanda ke diban cewa ba wanda zai iya taimaka masu ga kai ga gurin su a zaman rayuwa.

KARANTA WANNAN KUMA; Wani Babban Jami’in Sojan Najeriya ya Kone a Gobarar wuta daga Hadarin Mota