Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumm’a, 24 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumm’a, 24 ga Watan Mayu, 2019

1. Hukumar ‘Yan Sanda sun tabbatar da Adamu Mohammed a matsayin IG na ‘yan sanda Najeriya

Hukumar ‘Yan sandan Najeriya, a ranar Alhamis da ta gabata ta tabbatar da sanya Adamu Mohammed a matsayin shugaban ‘Yan sanda (IGP).

An gabatar da shi ne a wata taron majalisar ‘yan sandan da shugaban Muhammadu Buhari ya jagoranta.

2. Kotu ta bada ranar da za a ji Karar Saraki da Hukumar EFCC

Babban Kotun Koli na Tarayyar dake zaune a Abuja za ta ji wata karar da Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki zai gabatar a ranar 24 ga watan Yuni, akan kalubalantar hukumar EFCC.

Babban kotun tarayya ta makon da ta gabata ta umurci EFCC da sauran hukumomin da su dakatar da zarge-zargen cin hanci da rashawa akan tsohon gwamnan Jihar Kwara.

3. ASUU na barazanar fara sabon yajin aiki

Bisa rahotanni da aka bayar ga Naija News, Kungiyar Malaman Babban Jami’o’i (ASUU) na bada alamun aiwatar da sabon yajin aiki a Makarantu.

An gane da hakan ne bisa wata sanarwa da ‘yan kungiyar ke yi da cewa kada a ga laifin membobin kungiyar idan sun fara kauracewa hidimar koyaswa a Jami’o’i.

4. Kotun Karar Zabe ta yi watsi da gabatar wan HDP na dakatar da hidimar rantsar da Buhari

Kotun Koli da ke jagorancin karar zabe ta gabatar da yin watsi da karar da Jam’iyyar HDP suka gabatar na neman cewa kada a gudanar da hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya, kamar yadda aka sanar da yin hakan ga ranar 29 ga watan Mayu 2019.

Naija News Hausa ta sanar a baya a wata sanarwa cewa dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar HDP a zaben 2019, Mista Ambrose Aworu, ya bukaci Kotu da dakatar da hidimar ranstar da Buhari a karo ta biyu ga shugabanci.

5. Osinbajo ya jagorancin taron bankwana da Kungiyar NEC

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilci shugaba Buhari da jagorantar taron majalisar dinkin duniya na kasa da kasa (NEC) a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja.

Yawancin gwamnonin jihohi sun halarci taron, a yadda taron na zamanan taro na karshe ga wadansu daga cikin Gwamnonin don sassar su zai ƙare a ranar 29 ga Mayu, 2019.

6. An zabi Fayemi da zaman Ciyaman na Kungiyar Gwamnonin Najeriya

Gwamna Kayode Fayemi, Gwamnan Jihar Ekiti a ranar Laraba ta da wuce ya lashe zaben jagorancin kwamitin Gwamnonin Najeriya (NGF) na tsawon shekaru biyu.

Haka kazalika aka zabi Gwamna Aminu Tambuwal daga Jihar Sakkwato a matsayin mataimakin shugaban kungiyar.

7. PDP: Atiku Abubakar ya bayyana wata makirci da ake akan sa

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa wasu mutane na kadamar da yin makirci akan sa da manyan shugabannai a Jam’iyyar PDP don bata masu suna.

Atiku ya gabatar da hakan ne cikin wata sanarwa da aka aika a ranar Alhamis ga Naija News.

8. Hukumar Kwastam sun kwace Kwantenan 2 na Fatar Jaki a Legas

Jami’an Hukumar kwastam sun bayyana fata dabbobi, musanman Jakkuna a matsayin kayakin da hukuma ta hana warwashi da su don tana a karkashin kariyar fitarwa, da nufin hana dabbobi daga karewa a kasar.

Bisa bayanin Hukumar Kwastam na Jihar Legas, sun bayyana da cewa Kwantena biyun da suka amshe zai kai akilla naira biliyan goma sha biyar (N15billion), idan an sayar da su.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com