Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Shugaba Buhari zai ziyarci Jihar Gombe a yau don wata Kadamarwa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Naija News Hausa, Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Labaran Najeriya a Yau, Labaran Hausa, Shugabancin Kasar Najeriya

Naija News Hausa ta karbi rahoto cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar Gombe a yau Litini don wata hidimar kadamarwa a jagorancin Ibrahim Dankwambo, Gwamnan Jihar Gombe.

An riga an watsar da darukan tsaro kamin isar shugaban a Jihar don hana wata tashin hankali ko harin ‘yan ta’adda a hidimar.

Ga kadan daga cikin ayukan da shugaban zai je kadamarwa a Jihar; Gidan Cibiyar Tattaunawar Tarayyar Kasa, Kofar Shiga Jihar Gombe da kuma Garejin Motocin Tanki da ke a hanyar Bauchi, Asibitin Mata da Yara, da kuma wasu Hanyoyi da Gwamna Dankwambo ya tsarafa a Jihar.

Haka kazalika da Makarantar Jami’a ta Kiwon Lafiya (College of Medical Sciences of the Gombe State University) hade a Makarantar Firamare ta Santirar Gombe, da dai sauransu.

Alhaji Umar Ahmed, Kwamishanan Jihar ya gargadi jama’ar Jihar, Mata da Maza, Yara da Manya da fita don marabtan shugaba Muhammadu Buhari da kuma ganawa da hidimar.

KARANTA WANNAN KUMA; Kalli Bidiyon Salisu Mu’azu, Shahararran Mai Hadin Fim a Kannywood, bayan da ‘Yan Fashi suka sake shi.