Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 27 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 25 ga Watan Mayu, 2019

1. Aisha Buhari ta kalubalanci Gwamnatin Najeriya da kashe dala Miliyan $16m akan Gidan Sauro

Matan Muhammadu Buhari, Shugaba Kasan Najeriya, Aisha Buhari ta sauya wa Gwamnatin Tarayyar kasar da kashe kudi kimanin dala miliyan goma sha shidda akan sayan gidan sauro.

Naija News ta fahimta da bayanin Aisha ne bisa wata gabatarwa da ta yi a wani zaman tattaunawa da Mata a Gida Majalisar Kasar Najeriya, Abuja, ranar Asabar, 25 ga watan Mayu da ya gabata.

2. APC: Dan Takaran Gwamna a Jihar Bauchi daga Jam’iyyar shugabanci, Yakubu Lame ya Rasu

Tsohon Ministan Harkokin ‘Yan Sanda da kuma dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2019 daga Jam’iyyar APC, Dakta Ibrahim Yakubu Lame ya rasu a karshen makon da ta gabata.

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa Dakta Lame ya rasu ne a wata Asibitin da ke a birnin Abuja, a daren ranar 25 ga watan Mayu, Asabar da ta wuce.

3. Hukumar INEC ta bayyana ranar da zata bada Takardan Yancin Mulki ga sabon Gwamnan Zamfara

Hukumar Kadamar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya (INEC) ta gabatar da cewa ranar 27 ga watan Mayu ne zata bada takardan yanci da shugabanci ga Gwamnan Jihar Zamfara da mataimakin sa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kotun Koli ta tsige Gwamnan Jihar Zamfara daga Jam’iyyar APC, ta kuma gabatar da dan takara daga Jam’iyyar PDP a matsayin mai nasara ga zaben Jihar.

4. Gwamna Yari da Jam’iyyar APC ta Zamfara sun Amince da Shari’ar Kotu

Abdulaziz Yari Abubakar, Gwamnan Jiahr Zamfara da manyan mambobin Jam’iyyar a Jihar Zamfara sun dauki kaddara da amince da Shari’ar da Kotu ta gabatar akan shugabancin Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatarwa ga mabiya bayan Jam’iyyar APC a Jiahr, a garin Gusau da cewa sun amince da daukar kadara akan zancen Kotu na gabatar da dan takaran PDP a matsayin wanda ya dace da shugabancin Jihar.

5. Kotun Karar Zabe ta yi Watsi da Karar PDP a Jihar Filato

Hukumar zaben Jihar Filato a ranar Asabar da ta wuce, ta gabatar da yin watsi da kara da zancen Jam’iyyar Adawa (PDP), akan kalubalantar nasarar APC a karamar hukumar Arewacin Langtang, a Jihar Filato.

Ka tuna cewa dan takaran kujerar Ciyaman na karamar hukumar Langtang daga Jam’iyyar PDP, Ubandoma Joshua-Laven, ya kalubalanci Hukumar INEC da gabatar da dan takaran Ciyaman na hukumar daga Jam’iyyar APC, Kparnim Nanloh-Amos, a matsayin Ciyaman na Langtang ga hidimar zaben ranar 10 ga watan Aktoba a shekarar 2018 da ta gabata.

6. Gwamnan Jihar Adamawa na barazanar daukar matakai ga ‘Yan Siyasar Jihar

Sabon Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Fintiri, ya bayyana da cewa yana a shirye don daukan matakai da yaki da matsalolin da Jihar Adamawa ke fuskanta.

Naija News Hausa ta fahimta cewa Gwamnan ya bayyana da cewa bai damu ba da yiwa wasu laifi ba a Jihar, musanman ‘yan siyasa, don tabbatar da cewa ya magance matsalolin Jihar.

7. Aisha Buhari tayi sabon alkawari ga Mata da Matasa kamin ranar rantsar da Buhari

Matan shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta sake gabatar da sabon alkawali ga Mata da kuma matasa da cewa zata tababatar da ganin sun samu shiga harkan shugabanci a kasar Najeriya.

Aisha ta gabatar ne da hakan a ranar Asabar da ta wuce, a wata ganawa da ta yi da wasu shugabannan Matan Najeriya, a nan fadar shugaban kasa, Abuja.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com