Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Shugaba Muhammadu Buhari zai yi gabatarwa ga ‘yan Najeriya a Yau

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

”Yan Kwanaki kadan ga hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasan Najeriya a karo ta biyu, a yau 27 ga watan Mayu 2019, shugaban zai yi gabatarwa ga al’ummar Najeriya a wata tattaunawa da za a nuna a Gidan Talabijin na NTA.

Naija News Hausa ta fahimta da wannan gabatarwan ne bisa sanarwan da Mista Femi Adesina, Mashawarci ga Buhari ta al’amarin sadarwa ya bayar a yau ga manema labarai.

Za a nuna hidimar gabatarwan shugaba Muhammadu Buhari ne a missalin karfe goma (10PM) na daren ranar yau Litini.

An kara bayyana da cewa wasu Gidan Talabijin da dama kuma zasu nuna gabatarwan, saboda haka ana gargadin duk dan Najeriya dake muradin kallon hidimar ya juya a layin Talabijin na shi a NTA ko wani Gidan Talabijin, a missalin karfa goma na daren yau.