Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na ganawar Kofa Kulle da Gwamnonin Jiha

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari a yau Litini, 27 ga watan Mayu na ganawa da Gwamnonin Arewacin Jihohin kasar Najeriya a nan fadar shugaban kasa, birnin Abuja.

Ko da shike ba a bayyana ko menene dalilin taron gaggawar ba, amma manema labarai na hangen cewa ba zai wuce yanayin matsalar hare-hare da ake fuskanta ba a kasar, musanman Arewacin kasar.

Naija News Hausa na da sani da fahimtar cewa kashe-kashen rayuka na yaduwa a koyaushe a arewacin kasar Najeriya, musanman daga ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma Makiyaya Fulani.

Ka tuna a hangen magance hakan ne hukumar Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya suka kafa wata rukunin Tsaro da suka kira ‘Operation Puff Adder’, duk da hakan matsalar harwayau bai bai sauya ba a kasar.

Bisa rahotannai, a ranar jiya Lahadi, an rasa rayukan mutane da gidajen zama a shiyar Dutse Uku, Rikkos da kuma Gadar Cele ta garin Jos, Jihar Filato, a wata sabuwar harin da ‘yan ta’adda suka kai.

Taron shugaban kasar da Gwamnoni Arewacin kasar ya samu halartan Gwamnoni kamar su; Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna; Kashim Shetima, Gwamnan Jihar Borno; Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi; Simon Lalong, Gwamnan Jihar Filato; Aminu Tambuwal, Gwamnan Jihar Sokoto; Atiku Bagudu, Gwamnan Jihar Kebbi da kuma Abubakar Sani Bello, Gwamnan Jihar Neja.