Connect with us

Uncategorized

Mutane 5 sun Mutu a Farmakin da ya tashi tsakanin Dutse Uku da mutanen Angwan Damisa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Najeriya ta Jihar Filato ta sanar da wata farmaki da ya tashi tsakanin mazaunan shiyar Dutse Uku da Angwan Damisa, ta karamar hukumar Areacin Jos, inda aka kashe mutum 5 da kone gidaje kusan goma sha biyu a Jihar.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar Filato, Tyopev Terna, a wata sanarwa da ya bayar a ranar Litini da ta gabata, ya bayyana da cewa farmakin ya tashi ne tsakanin mazauna kauyuka biyun sakamakon gawar wani mai suna Enock Monday da aka gano a daya daga cikin kauyan.

Mista Terna ya bayyana cewa da jin hakan Jami’an tsaro sun shiga kauyan don daukar Monday, suka kuma kai shi a wata Asibitin da ke a shiyar inda daktan asibitin ya bada tabbacin cewa lallai ya riga ya mutu.

Sanarwan Mista Terna din na kamar haka;

“A ranar 26 ga Mayu 2019, a missalin karfe 11:30, jami’an tsaro sun karbi wata kira daga Sarki Arum da ke wakilcin shiyar Tina a karamar hukumar Arewacin Jos, da cewa an gano da gangar jikin wani mai suna Enock Monday kwance a kasa tsakanin shiyar Dutse Uku da Angwan Damisa”.

“Anan take ne jami’an tsaro suka halarci wajen don daukar jikin Monday zuwa asibiti a inda aka bayyana da cewa lallai Monday ya riga ya mutu” inji shi.

Ya kara da cewa bayan da aka gane da mutuwar Monday sai farmaki ya tashi tsakanin kauyuka biyun, har ga kashe mutane biyar, aka kuma kone gidaje a kalla 12.