Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da Manyan Jami’an Tsaron Kasar Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Talata, 28 ga watan Mayu, shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da manyan shugabannan hukumomin tsaron Najeriya a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa zaman tattaunawar shugaba Buhari da jami’an tsaron ya fara ne a missalin karfe biyu na ranar yau, akwai ganewa da cewa ganawar ya kasance ne don tattauna akan matsalar tsaro a kasar.

Ka tuna mun sanar a wannan gidan labarai ta mu a baya cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ganawa da Gwamnonin Arewacin kasar a ranar Litini, 27 ga watan Mayu, a fadar shugaban kasa kan matsalar tsaro.

Wannan taron ya biyo ne sa’o’i kadan da lokacin da za a gudanar da hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu.

Har yanzu ana na kan tattaunawar a wannan lokacin da muke bayar da wannan rahoton, zamu kuma sanar da duk wata bayani da ta biyo baya a taron.

Ka bi wannan shafin don samun Labaran Siyasa na Najeriya a koyaushe.