Connect with us

Uncategorized

Akalla Mutane 7 suka mutu a karon Motar Dangote da wata Motar Bas a hanyar Jos

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton da wata mumunar hadarin Motar Dangote a babban hanyar Jos

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, a kalla fiye da mutane bakwai ne suka rasa rayukan su a lokacin da babbar Motar kamfanin Dangote ta fada wa wata Motar Bus ta Kamfanin ‘God’s Time is the Best transport company’ da ke a shiyar Jos.

Hadarin ya faru ne a ranar Talata da ta wuce a hanyar da ta bi Hawan zuwa Kibo, Jos.

An bayyana da cewa hadarin ya faru ne a yayin da birkin babbar motar kamfanin Dangote ya latse, Motar kuma ta sha karfin direban. A yayin jayayya da hakan ne ya rutsa cikin motar bus da ke tafowa a gabansa a kan hanyar.

Da ake karban bayanai, Ofisan Ilimi ga Hukumar Federal Road Safety Corps (FRSC), Mista Andrew Bala, ya bayyana cewa balagaggu ne mutane 13 da ke a cikin motar, Maza 10 da kuma Mata 3.

Ya kara bayyana da cewa an riga an kai mutanen da suka samu raunuka a Asibtin Salama hospital, da ke a Gidan-Waya. “An dauki gawakin mutanen da suka mutu, an kuma tafi da su a wajen ajiyar gawa a Asibitin Janara ta Kafachan, a Kaduna” inji shi.