Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Kalli Bidiyon Yadda aka kori Adams Oshiomhole wajen Rantsar da Shugaba Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Abin takaici ya faru a yau da Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar APC a hidimar neman zabe, Adams Oshiomhole, a yayin da ake gudanar da hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a birnin Abuja.

Ka tuna yau ne ranar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu ga farar fula, kamar yadda rahotannai da kuma Naija News ta sanar a baya.

A yau Laraba, 29 ga watan Mayu, a yayin da ake cikin hidimar rantsar da Buhari, an nuno lokacin da wani Jami’in tsaro ke tayar da Adams Oshiomhole daga kan layi inda sauran manyan Jami’an tsaro, manyan ‘yan siyasa, shugabannan Najeriya da kuma Shugaba Muhammadu Buhari ke tsayuwa.

Bisa ganewar Naija News Hausa, ba inda Adams Oshiomhole ya tsaya ya kamata ya tsaya ba a kan layin.

Bidiyon a halin yanzu ya mamaye ko ta ina a yanar gizon nishadi dauke da yadda aka kori Oshiomhole kamar wanda bai san abin da yake yi ba.

Kalli Bidiyon a kasa;