Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Kalli Hirar ‘Yan Najeriya a yayin da aka Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Najeriya a yau Laraba, 29 ga watan Mayu 2019, sun bi kan layi yanar gizon Twitter don yada yawun su ganin cewa an rantsar da shugaba Muhammadu Buhari ga shugabanci kasar Najeriya na tsawon shekara 4 a karo ta biyu ga farar fula.

Ka tuna da cewa Hukumar INEC a zaben watan Fabrairun ta gabatar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga tseren takaran shugaban kasa ga zaben 2019.

A yau an rantsar da shugaban da kuma mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo, a yayin da kuma ake rantsar da Gwamnoni 29 a Jihohin kasar.

Shugaba Buhari a lokacin da yake gabatarwa a hidimar rantsarwan, ya kara alkawari ga al’umar Najeriya da cewa zai yi iya kokarin sa don shugabancin da ya dace, “Ba zani yadda son kai ya maye zuciya na ba wajen jagoranci da mulkin kasar Najeriya ba, zan kuma ci gaba da shugabanci na ta hanyar da dokar kasar ta bayar” inji Buhari.

A bayan da shugaban ya gama gabatarwan sa, aka kuma rantsar da shi, ‘yan Najeriya sun bi layin yanar gizon nishadi ta Twitter don bayyana ra’ayin su ga komawar shugaban kan mulki a karo ta biyu.

Kalli sakonnan kamar haka a layin Twitter kamar yadda aka aika shi a turance;