Connect with us

Uncategorized

Hukumar EFCC sun kame dan Uwan Shinkafi da Naira Miliyan 60 cikin Mota

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Talata da ta gabata, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kuma kare Tattalin Arzikin kasar Najeriya (EFCC) ta Jihar Sokoto sun kame wani dan siyasa da kudi naira Miliyan Sittin (N60, 000, 000).

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Hukumar sun gane da shi ne bayan da suka karbi wata kirar kula na gaugawa daga wata liki.

EFCC sun kame dan siyasar, Murtala Muhammad da ake zargi da zama dan uwa ga Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Farfesa Abdullahi Shinkafi, a wata shiya mai lamab 145 Igala Housing Estate, Off By-pass Road, a Gusau, Jihar Zamfara.

An kame shi ne da wata Bakar Motar Toyota Land Cruiser Prado Jeep mai lamba DKA 67 PX Kaduna, dauke da buhunan Ghana Must go 4, kowane cikke da jerin naira dubu daya a cikinta. An bayyana cewa kowane buhu na dauke ne da Miliyan Goma shabiyar, a jimila motar da dauke da Miliyan Sittin (N60,000,000).

A cikin motar kuma an gane da wata Doguwar Bindiga guda, Da wata karamar Bindigar Fisto, hade da kuma jerin arsasun bindiga mai tashi goma shabiyu da wasu miyagun makami kuma duk a cikin motar.

A halin yanzu ana kan bincike ga al’amarin, kuma za a mikar da shi a kotu bayan an kamala bincike.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Hukumar Kwastam sun kwace Motar Kwantena 2 cike da Fatar Jaki a Jihar Legas.