Connect with us

Labaran Najeriya

Buhari da Tsohin Shugabannan Najeriya sun Kauce wa Liyafa a Fadar shugaban kasa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaba Muhammadu Buhari, hade da wasu Tsohon shugabannan kasar Najeriya sun kuace wa hidimar Liyafa da aka gudanara a daren ranar Laraba da ta gabata a birnin Abuja don murna da hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a shugabanci na karo ta biyu.

Ko da shike tsohon shugaban kasar, Yakubu Gowon ya samu halartan hidimar da aka yi a nan gidan gwamnatin tarayyar kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Duk da yadda ake zato da kuma neman bayyanar tsohin manya da suka shugabanci kasar a baya, amma hakan bai samu ba, a yadda tsohin shugabannai kamar su Olusegun Obasanjo, Dakta Goodluck Jonathan, Janar Ibrahim Babangida, Chief Ernest Shonekan da Janar Abdusalami Abubakar suka kaurace wa hidimar liyafar.

A bayanin Babban Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya (SGF), Boss Mustapha ya fada da cewa hidimar rantsarwa da aka yi wa Buhari ya bayyana sabon shiri da matakin shugabanci da aka rataya wa shugaban don jagorancin kasar a karo ta biyu a tsawon shekaru hudu ta gaba.

A haka kazalika, Ciyaman na Tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya nuna godiya ga al’ummar Najeriya ga goyon bayan su da kuma bangaskiyar su da gwamnatin. “Wannan babban nasara ne da ci gaba ga al’ummar Najeriya gaba daya” inji Oshiomhole.