Connect with us

Labaran Najeriya

Bamu kame Okorocha ba – inji Hukumar EFCC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kare Tattalin Arzikin kasar Najeriya, EFCC sun yi watsi da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizo a ranar Alhamis da ta wuce da cewa sun kame tsohon Gwmanan Jihar Imo, Rochas Okorocha da Matarsa.

Kamar yadda muka sanara a baya a Naija News Hausa da cewa bamu da tabbacin kame Okorocha, amma zamu sanar da duk wata hira da ya biyo zancen.

Shugaban Hukumar EFCC, Mista Ibrahim Magu, ya mayar da martani ga rahotannai da cewa lallai hakan ba gaskiya bane, hukumar ba su kame Okorocha da Matarsa ba ko kuma ‘yan uwansa.

”Ba gaskiya bane, bamu kame Gwamna Rochas Okorocha ba” inji Magu.

Da aka tugumi Ibrahim Magu ko wata kila hukumar EFCC na kadamar da bincike akan Gwamnan, ya amsa da cewa “Tabas akwai bincike akan Tsohon gwamnan”

KARANTA WANNAN KUMA; Kalli Bidiyon Yadda aka kori Adams Oshiomhole wajen Rantsar da Shugaba Buhari