Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli Hotunan Lokacin da Shugaba Buhari da Iyalin sa ke Nishadewa bayan hidimar Rantsarwa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta gano da hotunan yadda shugaba Muhammad ke washewa da murna bayan da aka gama hidimar rantsar da shi a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu da ta gabata a matsayin shugaban kasan Najeriya a karo ta biyu ga mulkin farar fula.

Ko da shike Jam’iyyar Adawa da dan takaran su ga tseren kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga PDP, Alhaji Atiku Abubakar na jayayya da nasarar Buhari a Kotun Neman Yanci.

Amma da samun kai ga yin hidimar rantsarwa, Shugaba Muhammadu Buhari bai da wata alamar jijjiga ko damuwa ga lamarin karar ko shari’ar da Kotun Neman yanci zata gabatar ga zancen.

Shugaba Buhari da Iyalin sa sun cika da murna kwarai da gaske ganin an kamala rantsar da shugaban ba tare da wata tashin hankali ba.