Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 31 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 31 ga Watan Mayu, 2019
1. Sanata Ademole Adeleke ya ci nasarar kara a Kotu
Sanatan da ke wakilci a Jihar Osun, Ademola Adeleke ya samu yanci takara ga hidimar zaben Jihar Osun ta watan Satumba 2018.
Katuna a baya kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa cewa Kotun Kara ta Abuja a jagorancin Alkali Othman Musa na Kotun Koli ta Bwari, Abuja, ya gabatar da tsige Ademola Adeleke daga daman cika dan takara ga zaben tseren kujerar Gwamna da aka yi a Jihar Osun, Watan Satumb 2018.
2. Tsohon Minista a karkashin Buhari ya bukaci Oshiomhole da barin kujerar sa na Ciyaman APC
Tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu yayi kira ga Ciyaman Tarayya na Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da barin kujerar jagorancin Jam’iyyar.
Ka tuna cewa mataimakin Ciyaman na Jam’iyyar APC kuma daga Arewacin kasar Najeriya, Sanata Lawal Shuaibu, shi ma ya bukaci Oshiomhole da yin hakan.
3. Hukumar EFCC tayi watsi da zancen kame Okorocha da Matarsa
Kamar yadda muka sanar a ranar jiya da jita-jitan da ya mamaye layin yanar gizo da rahotannai cewa Hukumar EFCC sun kame tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha da Matarsa hade da ‘yan uwansa da ke zama da shi, Hukumar sun gabatar da cewa hakan bai faru ba.
Ka tun da cewa Hukumar INEC sun ki baiwa Okorocha takardan yancin wakilci a gidan Majalisa duk da cewa ya lashe zaben 2019 a gidan Majalisar Dattijai.
4. Kotu ta baiwa Naira Marley belin Naira Miliyan Biya (N2 million)
Kotun Koli ta Ikoyi, a Jihar Legas, babban birnin kasuwancin kasar Najeriya, ta bada daman beli akan kudi naira Miliyan 2 ga wani mawakin Hipop a Najeriya mai suna Azeez Fashola da aka fi sani da likin suna Naira Marley.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Hukumar EFCC ne ta bada umarnin kame Naira Marley a kwanakin baya, da zargin halin da bai dace ba da kuma ta karya dokar kasa.
5. Bayanin diyar Atiku game da aiki a karkashin Jam’iyyar APC
Dakta Fatima Atiku, diyar dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar APC a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ta bayyana dandanon ta da kwarewa a lokacin da ta yi aiki a karkashin Gwamnan Jam’iyyar APC.
Naija News Hausa na da ganewar cewa Fatima ta yi aiki ne a matsayin Minista Kula da Lafiyar Jiki a karkashin tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Muhammadu Bindow.
6. Kotu ta Tsige Mista Ned Nwoko daga kujerar Sanata
Kotun Karar zabe ta birnin Tarayya, Abuja ta tsige Mijin Regina Daniels, ‘Yar Wasan Fim na Turanci a Najeriya, Mista Ned Nwoko daga kujerar Sanata a karkashin Jam’iyyar PDP.
Gidan labaran nan tamu ta gane da cewa Kotun ta dakatar ne da Nwoko daga kujerar Sanata na Wakilcin Arewacin Jihar Delta.
7. Majalisar Dinkin Duniya ta Jam’iyyar APC tayi ganawa da Manyan Jam’iyyar
Manyan Jam’iyyar APC da Majalisar Dinkin Duniya ta Jam’iyyar tayi kirar gaugawa da Kwamitin Aikace-Aikacen Tarayyar Kasa (NWC) na Jam’iyyar.
A fahimtar Naija News, Jam’iyyar da Kwamitin sun yi wannan kirar gaugawa ne da tattaunawa akan tsananci da wasu manya daga Jam’iyyar ke yi na bukatar cewa ciyaman na Jam’iyyar, Adams Oshiomhole ya janye daga kujerar jagoranci.
8. Kakakin Yada Yawun Majalisar Jihar Imo yayi murabus da kujerar sa
Sabon dan Majalisa da kuma Kakakin yada yawun Majalisar Jihar Imo, Hon. Lawman Duruji, a ranar Alhamis da ta gabata, ‘yan sa’o’i kadan da shiga Ofishi, yayi murabus da kujerar sa.
Hon. Duruji ya shiga Ofishin ne bayan da tsohon kakakin Majalisar, Acho Ihim ya dakatar da kansa daga wakilci da jagorancin Majalisar.
Ka samu kari da Cikakken bayani game da Labaran Najeriya a Shafin Hausa.NaijaNews.Com