Connect with us

Labaran siyasa

Sabon Gwamnan Jihar Yobe, Buni ya Auri diyar tsohon Gwamnan Jihar rana ta biyu da rantsar da shi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Yobe ya kara Mata guda bisa biyu da yake da su a da

Naija News Hausa ta  karbi rahoto da cewa sabon gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da aka rantsar ga kujerar Gwamna a ranar Alhamis, 29 ga Mayu 2019 da ta gabata ya kara Aure rana ta biyu ga rantsar da shi.

Bisa fahimtar gidan labaran nan tamu, yarinyar mai suna Ummi Adama Gaidam, diya ce ga tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Ibrahim Gaidam.

A halin yanzu, bincike ta nuna da cewa yarinyar na kasar Saudi Arabia tana karatu, idan kuma ta kamala sai ta dawo da zama matar Gwamnan ta Uku.

Bisa bayanin wani da ke da cikakken sani ga lamarin, ya bayyana da cewa lallai Mista Buni ne ya nemi Ummi da Aure ba tare da sanin tsohonta ba, ko da shike wai yayi hakan ne don karfafa dankon siyasar shi da babban ta Gaidam.

Rahotannai sun bayar da cewa anyi auren ne a nan cikin gidan Malam Gaidam da ke a Sabon Fegi, Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

“An dauki duk matakai da ya kamata ga aure, harma da bayar da kwamdunan Goro dadai sauran su, aka kuma aurar da Fatima a gaban kanancin ‘yan uwan su” inji mai bada bayani, ko da shike yayi rokon cewa kada a gabatar da sunan sa”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya aika sakon Soyayya ga Matarsa Dolapo da nuna mata godiya, musanman yadda ta bashi hadin kai da nuna mashi so a shugabancin su ta farko.